Mataimakin gwamnan Zamfara, Mahdi ya tafka rashin kunya na ƙin bin Matawalle APC – Inji Fani-Kayode

0

Tsohon ministan Sufurin jiragen saman Najeriya, Frmi Fani-Kayode ya bayyana ƙin bin gwamnan Zamfara Bello Matawalle APC da mataimakin gwamnan sa Mahdi Gusau ya yi a matsayin rashin kunya babba.

Fani-Kayode jigo ne a jam’iyyar PDP sai dai kuma a ƴan kwanakinnan ya na gaba-gaba wajen bayyana a wasu daaga cikin sha’anonin jam’iyyar APC.

Na kwana-kwanan shine bayyana da yayi wajen bukin ɗaurin auren ɗan shugaban Kasa, Yusuf Buhari.

Idan ba a manta ba mataimakin gwamna Mahdi ya ki bin gwamnan jihar Bello Matawalle jam’iyyar APC yana mai cewa zai ci gaba da zama a jam’iyyar PDP ba zai bi gwamnan ba.

” Ƙin bin Matawalle APC da mataimakin gwamna Mahdi ya yi tsantsagwarra nuna tsagerancine da rashin kunya da nuna ba a tare. Idan ba zaman munafurci ya ke yi da Matawalle ba wanda shine gwamnan sa, kamata yayi ya goya masa baya su dunguma tare dukkan su su koma jam’iyyar APC amma yayi kememe ya ƙi.

Waɗannan kalamai na Fani-Kayode ya jawo cece kuce a tsakanin mutane, inda wasu ke ganin bai kamata ace yana ɗan Jam’iyyar PDP ya fito yana furta irin waɗannan kalamai ga ɗan jamiyyar sa.

Jihar Zamfara na fama da ruɗaninb hauragiyar siyasa, ba a jam’iyyar APC ba hatta a jam’iyyar PDP.

Su kan ƴannAPC din ba su zaman lafiya a tsakanin su inda tsohon gwamnan jihar AbdulAziz Yari, Sanata Kabiru Marafa da Sanata Ahmed Sani Yeriman Bakura ke jani-in-ja ka tsakanin su da gwamnan jihar Matawalle kan wa ye zai jagoranci jam’iyyar a Jihar.

Share.

game da Author