Mata sun fi maza yawan waɗanda ke ɗauke da cutar ƙanjamau a Najeriya

0

Wani rahoto ya tabbatar da cewa yawan matan da su ka kamu da cutar ƙanjamau ya ƙaru sosai tsakanin shekarun 2016 zuwa 2019.

Haka nan kuma rahoton ya nuna cewa yawan maza masu kamuwa da cutar ta HIV/Aids ya ragu sosai tsakanin shekarun na 2016 zuwa 2019.

Cibiyar Binciken Adadin Masu Ɗauke da Cutar Ƙanjamau (NAIIS) wadda ta yi wannan bincike cikin 2018, ya nuna cewa akwai mutum kimanin miliyan 1.9 ‘yan ƙasa da shekaru 64 ke ɗauke da cutar ƙanjamau.

Amma wani rahoton baya-bayan nan da Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ta fitar, ya nuna cewa rabin masu ɗauke da cutar ƙanjamau a Najeriya duk mata ne.

Rahoton ya ƙara da cewa mata sun ƙaru da cutar ƙanjamau daga kashi 53.1 cikin 2016 zuwa kashi 55.5 cikin 2017. Sai kuma kashi 55.83 cikin 2028 da kuma kashi 56.03 cikin 2019.

Amma kuma yawan maza masu kamuwa da cutar ƙanjamau ya na raguwa a waɗannan shekaru uku a jere, daga 46.9 cikin 2016 zuwa kashi 44.5 cikin 2017 da kashi 43.97 cikin 2018 da 2019.

A ranar 25 Ga Agusta, 2021 ne Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ta fitar da ƙididdigar.

Share.

game da Author