Masallatai 11, Coci-Coci 4 Zulum ya rusa a Maiduguri – Kungiyar Muric

0

Ƙungiyar Muric dake Kare hakkin Musulunci a Najeriya ta karyata korafin wasu kungiyoyin Kiristocin jihar Barno cewa wai gwamnan Barno, Babagana Zulum da gangar yake rusa wuraren ibadan Kiristoci saboda kiyayya a jihar.

Idan ba a manta ba tun bayan rusa cocin EYN a Maiduguri, Kiristocin Barno suka rika sukar gwamnatin jihar da hukumar raya birane na jihar suna cewa da gangar gwamnati ke rusa wuraren Ibadan Kiristoci a jihar saboda nuna kiyayya ga mabiya addinin a jihar.

Sai dai kuma kungiyar Muric kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito ta yi tattaki harzuwa garin Maiduguri domin yin binciken tabbatar da ainihin abinda gwamnati ke yi a jihar da bin diddigin wannan korafi na Kiristocin jihar.

” Mun garzaya har ofishin hukumar raya birane na jihar Barno BOGIS inda muka gano cewa ashe abin ba kamar yadda ake yaɗawa bane suke, masallatai har 11 aka rusa coci 5, kuma duk sun karya dokar hukumar BOGIS.

Mun gano cewa zuwa yanzu gwamnati ta rusa masallatai har guda 11 a fadin jihar a kokarinta na bunƙasa garin Maiduguri. Hakazalika Coci biyar ne aka rusa zuwa yanzu a wannan aiki da hukumar ke yi.

” Ba gaskiya bane yaɗawa da ake yi da korafe-korafen kungiyar Kiristoci wai gwamnnan jihar Zulum wuraren ibadan Kiristoci ne kawai ya ke rusa.

Muric ta ce ta bi wuraren da aka rusa ɗaya bayan ɗaya domin ta tabbatar da abinda ake faɗi.

Ta kara da cewa duka unguwannin da aka rusa masallan da coci-cocin duk sun je kuma sun tabbatar da gaskiyar gwamnati da abinda take yi a jihar.

” Duk ginin da aka rusa ya karya doka, wasu basu da takardun mallakan waɗannan filaye, wasu kuma sun gina ba a inda ya kamata ba ko kuma aka basu da farko.

” Muna kira ga mutane su dai kawo ruɗani a kan abinda ba su sani ba. Sannan su dai tada jijiyoyin wuya kan wani abu na son rai irin na su. Gwamnatin Barno na aiki, rokon mu shine a kyale gwamna Zulum ya ci gaba da ayyukan gyara da yake yi domin ci gaban jihar.

Share.

game da Author