MARTANIN APC GA JEGA: Ayyukan raya ƙasar da Buhari ya yi sun wuce na PDP fintinkau

0

Jam’iyyar APC ta ragargaji tsohon shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, Farfesa Attahiru Jega, wanda ya bayyana cewa da APC da PDP duk jirgi ɗaya ya kwaso su, Jummai da Jummala ne.

A cikin tattaunawar da Jega ya yi da BBC Hausa a ranar Litinin, ya yi kira ga ɗaukacin ‘yan Najeriya su watsar da APC da PDP a bola, su rungumi wata jam’iyya mai mutane nagari a zaɓen 2023.

APC DA PDP Jummai Da Jummala Ne -Jega

Farfesa Attahiru Jega ya kwatanta jam’iyyar PDP da APC kamar wasu tagwaye ‘yan gida ɗaya, ciki ɗaya kuma masu kama ɗaya.

Ya kwatanta su da wasu girɗa-girɗan tagwayen da ke kama da juna wajen wawurar dukiyar ƙasar nan, su ka kuma kasa warware matsalar tattalin arzikin ƙasar nan tsawon shekaru 20.

APC Da PDP: Bai Kamata ‘Yan Najeriya Su Sake Bai Wa Kuraye Amanar Ƙasar Nan Ba -Jega

“Mummunar ‘illar da AOC da PDP su ka yi wa ƙasar nan, ta yi munin da ganganci ne da kuma babban kuskure idan har aka sake bai wa ɗaya daga cikin amanar mulkin ƙasar nan. Kai har abada ma bai kamata a sake ba su amana ba. Saboda a fili sun nuna ba za su taɓa canjawa ba.

“APC da PDP sun kafa gwamnati, kowa ya shaida cewa ba su zo da kyakkyawar manufa ba. Duk yawancin ɓarayin gwamnatin da ya kamata a ce su na kurkuku duk sun laɓaɓa sun shige cikin APC.”

Jega ya yi kiran da a rungumi PRP jirgin tsira.

Share.

game da Author