Wasu hasalallun mambobin jam’iyyar APC su 100, sun maka Shugabannin Riƙon Jam’iyyar APC ƙarƙashin Gwamna Mala Buni kotu.
A ƙarar wadda su ka shigar a Babbar Kotun Tarayya, Abuja, mutanen su 100 sun nemi kotu ta bayyana haramcin kwamitin shugabancin APC na ƙasa, bisa dalili da hujjar cewa:
1. Mambobin Shugabannin Riƙo su 13, alhali kuma doka cewa ta yi Shugabannin Riƙo kada su kasa kai 24, kuma kada su wuce 24.
2. Doka cewa ta yi a kafa mambobin Kwamitin Shugabancin Riƙo su 24 kuma su fito daga aƙalla kashi 2/3 na jihohin Najeriya 36 da FCT Abuja. Amma shugabannin riƙon APC ba a haka aka naɗa su ba.
3. Dokar Najeriya Sashe na 183 da Dokar APC Sashe na 17 (4), sun haramta wa Gwamna ya riƙe muƙamai biyu a lokaci ɗaya. Shi kuma Gwamna Buni ya karya wannan dokar.
4. Ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/938/2021, ta ce babu inda doka ta amince MInistan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami ya rantsar da Shugaban Riƙon APC. Don haka wannan rantsuwa ba ta da bambanci da kirari ko kambamawa, ba rantsuwa ba ce, harmtacciya ce.
PREMIUM TIMES dai ta ci karo da kwafen takardun bayanan ƙarar, wadda lauya Samuel Irabor ya shigar, a madadin mambobin APC ɗin su 100.
A ƙarar dai an haɗa da sunan Malami da Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC), an maka kotu.
A wata sabuwa kuma, jam’iyyar PDP a jihar Yobe ita ma ta maka Gwmna Buni ƙara Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, inda ta ke neman a tsige shi da mataimakin sa a naɗa ɗan takarar PDP da na sa mataimakin.
PDP ta ce naɗa Buni riƙon APC ya karya dokar rantsuwar da aka yi masa ta Gwamna a Jihar Yobe.
PREMIUM TIMES ta ga wannan kwafen ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/885/2021 a ranar Alhamis.
Idan ba a manta ba, manyan jiga-jigan APC sun yi nuni da cewa Gwamna Buni ba shi da halascin riƙe jam’iyyar APC, don haka duk wani zaɓen da za’a gudanar a ƙarƙashin sa, idan APC ta yi nasara za a iya ƙwacewa.