Gwamnatin jihar Neja ta bayyana cewa kashi 39.1 cikin 100 na matan jihar ne ke shayar da jariran su nonon uwa zalla na tsawon watanni shida.
Kwamishinan lafiya na jihar Muhammad Makusidi ya sanar da haka a taron wayar da kan mata sanin mahimmancin shayar da jarirai nono zalla na tsawon watanni shida da aka yi a garin Minna ranar Talata.
Makusidi ya koka da karancin kason matan dake shayar da jarirai nono zalla a jihar yana mai cewa dole gwamnati ta mike tsaye wajen kawo karshen wannan matsala.
Ya ce gwamnati za ta ware kudade domin wayar da kan mutane sanin mahimmancin shayar da jarirai nono zalla musamman mata.
“Gwamnati za ta inganta asibitoci domin karfafa gwiwowin mata masu ciki wajen zuwa yin awo.
Makusidi ya ce shayar da jarirai nono zalla hanya ce dake taimakawa wajen inganta lafiyar jariri tun yana yarao har zuwa ya girma.
Ya ce yin haka zai taimaka wajen kare su daga kamuwa da cututtuka masu kisa.
Sakamakon bincike da aka yi a Najeriya ya nuna cewa jariri daya ne tal cikin jarirai uku ke samun shayarwar nonon uwa zalla na tsawon watanni shida a kasar.
Binciken da cibiyar NNHS ta gudanar a 2018 ya nuna cewa har yanzu Najeriya na baya wajen shayar da jarirai nonon uwa.
Bisa ga binciken kashi 27 cikin 100 na jarirai ne kawai a kasar nan ake shayar da su nonon uwa zalla na tsawon watanni shida.
Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta yi kira ga duka sassan gwamnati kan kirkiro dokokin da zai taimaka wajen inganta shayar da jarirai nonon uwa zalla musamman na tsawon watanni shida.
Ta ce samar da doka irin haka ya zama dole ganin cewa shayar da jariri nonon uwa na samar wa yara kariya daga kamuwa daga cututtuka da kuma kare su daga yunwa.
Discussion about this post