Mai daki na ta yi barazanar sare min kai da adda don na hana ta daka da daddare – Kukan wani magidanci a Kotu

0

Wani magidanci mai shekaru 59, mai suna John Ifedinkor ya shaidawa Kotun Yankin Grade I a Kubwa, Abuja cewa matarsa, Ngozi na yi masa barazarar sare masa kai da adda kawai don ya hana ta yin daka da daddare a gidan su.

‘Yan sanda sun kama Ngozi bisa laifin tsorata mijinta.

Lauyan da ya shigar da karar Babajide Olanipekun, ya ce Ifedinkor ya fadi cewa Ngozi ta fara yi mijin ta barazarar kashe shi tun a ranar 13 ga Disambar 2020.

” A cikin dare daidai za mu kwanta barci sai Ngozi ta kunna risho kamar za ta dora girki. Da na tambaye ta sai ba ta amsa ni ba kawai kuma sai ta dauko turmi da tabarya ta fara daka. Cikin fushi sai na kwace tabaryar na hana ta dakar. ban an kara ba sai ta dauko adda ta zauna ta rika wasa shi, ashe wai kaina za ta sare, ta biyo ni da gudu.

Olanipekun ya bayan haka ne Ifedinkor ya kai kara ofishin ‘yan sandan dake Kubwa kan abin dake faruwa tsakanin sa da matar sa.

Olanipekun ya ce tun a baya dama akwai wasu lokuta da Ngozi ke yi wa mijinta da ‘ya’yan da suka haifa tare barazanar za ta kashe su ta hanyar zuba musu guba a abincin su.

Alkalin kotun, Muhammad Adamu, ya dage shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Oktoba.

Share.

game da Author