LAIFIN DAƊI: Messi ya yi sallama da Barcelona

0

Fitaccen ɗan wasan Barcelona, wanda yafi kowani ɗan wasa shahara a tarihin kungiyar ya yanke shawarar barin kungiyar Barcelona.

Duk da ko cewa kungiyar da ɗan wasan sun yarda a rage masa albashi, abin dai ya faskara, ba zai ci gaba da zama a Barcelona ba.

Duk wani abu da ake buƙatar ɗan wasa ya samu a kwallon ƙafa, Messi ɗan ƙasar Argentina ya samu a Barcelona kuma ita kanta Barcelonar ta samu a dalilin sa a kungiyar.

Wannan sanarwa da kungiyar da fidda a yammacin Alhamis ya tada wa mutane musamman magoya bayan ƙungiyar Barcelona da masoyan sa.

” Muna son Messi ya ci gaba da wasa a Barcelona, shima yana son ya ci gaba da wasa a ƙungiyar Barcelona amma kuma rashin kuɗi da dokar biyan albashin ƴan wasa ta Kasar Spain ya sa dole kungiyar da shi kansa Messi su hakura da juna.

” Babu yadda za mu yi sai dai mu yi wa Juna sallamar bankwana tsakanin mu da Messi.”

Share.

game da Author