KWALARA: Ta yi ajalin mutum 938 a jihohi 22 a Najeriya

0

Ministan muhalli Mohammad Mahmood Abubakar ya bayyana cewa kamata yayi gwamnati ta tsananta harkar wayar da kan mutane sanin illar dake tattare da kamuwa da cutar Kwalara sannan da wayar da kan mutane hanyoyin samun kariya daga kamuwa da cutar.

Abubakar ya ce sakamakon yaduwar cutar Kwalara da hukumar NCDC ta fitar ya nuna cewa cutar ta kashe mutum 938 a jihohi 22 da Abuja a kasar nan.

Jihohin Benue, Delta, Zamfara, Gombe, Bayelsa, Kogi, Sokoto, Bauchi, Kano, Kaduna, Plateau, Kebbi, Cross River, Niger, Nasarawa, Jigawa, Yobe, Kwara, Enugu, Borno, Kastina, Adamawa babban birnin tarayya Abuja na cikin jihohin da cutar ta barke a kasar nan.

Ya ce cutar ta barke ne a dalilin rashin tsaftace muhalli da yin bahaya a waje a jihar jihohin.

Abubakar ya ce hukumar za ta fara aikin wayar da kan mutane game da cutar da hanyoyin samun kariya domin dakile yaduwar ta a babbar birnin tarayya, Abuja.

Ya kuma yi kira ga mutane da masu ruwa da tsaki a fannin muhalli da su mike tsaye wajen ganin an tsaftace muhalli domin gujewa kamuwa da cutar.

Kwalara ta yi ajalin mutum 58 jihohin Taraba da Nasarawa

Akalla mutum 58 ne suka rasa rayukansu a dalilin kamuwa da cutar Kwalara a jihohin Nasarawa da Taraba.

A tsakanin watanni 8 din da suka gabata mutum 51 sun mutu a kananan hukumomi 8 a jihar Nasarawa sannan mutum 7 a kauyen Tella dake karamar hukumar Gassol.

Aruwan ya lakanta yaduwar cutar da rashin tsaftace muhalli da yin bahaya a waje.

A Taraba mutum 7 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar jihar Taraba.

Wani mazaunin jihar Taraba Ibrahim Halidu ya ce gwamnati ta aika da masu gudanar da bincike domin gano yadda cutar Gassol ta yadu.

Share.

game da Author