KWALARA A KADUNA: Mutum 1,665 sun kamu a Zaria, Kudan, da wasu kananan hukumomi 15 a jihar

0

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa an samu mutum 1,665 da suka kamu da cutar Kwalara a cikin watanni biyar da suka wuce a jihar.

Kwamishinar lafiyar jihar Amina Mohammed-Baloni ce ta fadi haka da take ganawa da manema labarai ranar Alhamis a Kaduna.

Mohammed-Baloni ta ce gwamnati ta samu rahoton cewa cutar ta barke a kananan hukumomi 19 a jihar daga watan Afrilu zuwa Agusta.

Kwamishinan ta alakanta barkewar cutar da rashin tsafta da tsaftace muhalli.

Ta ce kananan hukumomin da cutar ta bullo sun hada da Soba, Makarfi, Giwa, Chikun, Sabo gari, Zaria, Kaduna ta Arewa, Kachia, da Jaba.

Sauran, kananan hukumomin kuwa sun hada da Kubau, Lere, Sanga, Birin -Gwari, Kaduna ta Kudu, Kudan, Igabi da Kajuru.

Mohammed-Baloni ta ce gwamnati na kokarin ganin ta dakile yaduwar cutar musamman a wuraren da cutar ta fi tsanani.

” A Afrilun 2021 gwamnati ta samu rahotannin bullar cutar a wasu kananan hukumomi a jihar inda hakan ya sa ta aika da jami’an kariya domin daukan samfurin wadanda suka kamu da cutar domin yin gwaji.

“Daga cikin yawan mutanen da suka kamu da cutar mutum 842 sun warke sai dai har yanzu akwai mutum 14 dake kwance a asibiti.

Kwamishinar ta ce gwamnati ta bude asibitin kula da masu fama da cutar a duk kananan hukumomin da cutar ta bayyana.

“Mun zuba magungunan a duk asibitocin da muka bude domin kula da wadanda suka kamu da cutar sannan mun bada maganin chlorine domin tsaftace ruwan da mutane ke amfani da shi.

“Mun kuma aika da jami’an lafiya domin wayar da kan mutane sanin hanyoyin gujewa kamuwa da cutar, gudanar da bincike domin gano yadda mutane ke kamuwa da cutar da gano wadanda ke kamuwa da cutar.

A karshe Mohammed-Baloni ta yi kira ga mutane da su rika tsaftace muhallinsu da abincin da suke ci domin gujewa kamuwa da cutar.

“Mun san cewa kwalara cuta ce da aka fi kamuwa da ita a lokacin damina, haka ya sa muke kira ga mutane da su daina gina ban dakunan su kusa da rijiyoyin su kuma su maida hankulansu wajen tsaftace muhalli, jikinsu da abincin da za su ci.

Share.

game da Author