Gwamnan Jihar Katsina Aminu Masari yace baya jin daɗin kujerar gwamnan da ya ke akai saboda matsalar rashi tsaro da rashin tsaro da ya addabi kasar musamman jihar sa.
Gwamnan a wata hira da yayi da gidan radio na DW Hausa yace a kullum harkar mulki a Katsina tattare yake kalubalen tsaro kuma a kowane lokaci yana samun bayanai kan tsanani rashin tsaro daga kafofi da dama.
Masari ya bayyana cewa rashin tsaro ya kazanta ta inda har baya iya barci kuma baya jin daɗin hakan a matsayin shi na gwamna saboda babu wane shugaba da yake kishin al’ummarsa da zai samu kwanciyar hankali a irin wannan yanayi.
Wannan yanayi mai wuya ne matuka amma kuma wasu na ganin kamar ana jin dadi kawai.
Ya kuma kara da cewa a kullum barcin zomo yake yi da wayarsa a karkashin kunnensa saboda ko a cikin dare za a iya kiransa kuma duk wanda kaga ya Kiraka cikin dare ya kirakane ba wai saboda ya gai da ka bane sai dai don ya sanar da kai wata matsala.
Ya kamata mutane su daina yi kwa gwamna ganin wani mai jin daɗi ne ko kuma walwala.
Saboda idan jiniya ne ake yi wa gwamna, mai laifi ma idan za a kai shi gidan yari shima jiniya akeyi masa, mara lafiya ana yi masa jiniya, mamaci ma ana yi masa jiniya, har da yan kwana kwana suna jiniya idan wane mummaman abu ya faru.
Abinda yake da muhimmanci a shugabanci shi ne kada shugaba yabari giyar mulki yasa ya rika abinda bai dace ba kuma a koda yaushe ya rika tunanin akwai ranar da zai sauka daga wannan kujera.
Discussion about this post