Kotu ta yanke wa ɓarawon Ƙur’anin masallaci a Kano hukunci sharar masallaci Fage na wata ɗaya

0

Kotun Shari’a a Fage, Jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai suna Halifa Abdullahi hukunci sharar masallaci na tsawon wata ɗaya cur saboda satar Ƙur’anai 8 a masallaci.

Abdullahi wanda mazaunin rukunin gidaje na Kwatas ɗin Yola dake cikin birnin Kano ya ɓalle ƙofar masallaci a unguwar Tudun Maliki ya sace Ƙur’anai 8.

Alkalin Kotun, Bello Musa-Khalid, ya yanke wa Abdullahi hukunci sharar masallaci na wata ɗaya cur.

Ɗan sandan da ya kai ƙarar Abdullahi, Abdu Wada wanda shine ya karanta laifin ɓarawon Ƙur’an ya ce Abdullahi ya amince da laifin da ya aikata.

A dalilin haka Alkalin kotun ya yanke wa Abdullahi hukuncin ya rika share masallacin Juma’a na unguwar Fage na kwana 30. Wanda shine masallaci mafi girma a birnin Kano.

Share.

game da Author