Kotu a Kano ta yanke wa Nura Gwanda hukuncin kisa ta hanyar rataya

0

A ranar Alhamis ne babbar kotu a jihar Kano ta yanke wa Nura Gwanda mai shekaru 35 hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan ya kashe wani abokin sa mai suna Mudan Ibrahim mai shekaru 27 wuka.

Kotun ta kama Gwanda, mazaunin kwatas din unguwar Fagge a Kano da laifin kisa.

Alkalin kotun Aisha Ibrahim-Mahmoud, ta ce fannin shigar da kara sun tabbatar wa kotun cewa lalle Gwanda ya aikata lafin da ake tuhumarsa akai da hakan ya sa kotu ta yanke masa wannan hukinci.

Lauyan da ya shigar da karar Lamido Soron Dinki, ya ce Gwanda ya aikata laifin ne tun 6 ga watan Afrilun 2018 a kwatas din Fagge.

Ya ce a wannan rana wajen karfe 6 na yamma, Gwanda ya je gidan Mudan Ibrahim domin ya karbi wani bashin kudi har Naira 3,000 wanda dan uwan ibrahim ya ara a hannun Gwanda.

Soron dinki ya ce da Gwanda ya je gidan sai rashin jituwa ya shiga tsakani suka barke da cacan baki. Shi ko Gwanda da ya fusata sai ya zaro wuka ya caka wa Ibrahim a ciki da baya.

” An garzaya da Ibrahim asibitin Murtala Muhammad inda likita ya tabbatar cewa Ibrahim ya mutu tun kafin a iso da shi asibitin.

Sorondinki ya ce laifin da Gwanda ya aikata ya saba wa sashi na 221 na dokar manyan laifuka.

Sai dai Gwanda ya musanta aikata laifin.

Share.

game da Author