KORONA: Za a fara yi wa mutane allurar rigakafin cutar zango ta biyu ranar daga ranar 16 ga Agusta

0

Idan ba a manta ba a ranar Lahadi ne kwamitin PSC ta sanar cewa gwamnati ta dage ranar yi wa mutane allurar rigakafin cutar korona zango ta biyu.

Bisa ga takardar sanarwar wanda darektan yaɗa labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya Willie Bassey ya saka wa hannu Boss Mustapha ya ce gwamnati ta yanke wannan hukunci ne saboda wasu matsaloli da suka sha mata kai.

Kafin wannan lokaci dama kuma gwamnati ta sanar da ranar Talata 10 ga Agusta ranar da za a fara yi wa mutane allurar rigakafin zango ta biyu a asibitin FMC dake Jabi a Abuja.

Sai dai a safiyan Litini gwamnati ta sake fitar da sanarwar cewa za a fara yi wa mutane rigakafin Korona zango na biyu ranar 16 ga Agusta.

Shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ta ƙasa NPHCDA Faisal Shu’aib ya sanar da haka.

Shu’aib ya ce gwamnati ta dage ranar yin allurar rigakafin zango na biyu domin hukumar NPHCDA ta samu lokacin yin shirye-shiryen da ya kamata.

Allurar rigakafin korona a Najeriya

Idan ba a manta ba gwamnati ta fara yi wa mutane allurar rigakafin zango na farko ranar 5 ga Maris 2021 da ruwan maganin Oxford-AstraZeneca.

Zuwa yanzu mutum 3,938,945 ne suka yi allurar rigakafin korona a kasar nan.

Mutum 2,534,205 ne suka yi rigakafin a zango na farko sannan mutum 1,404,205 a zango na biyu
Gwamnati na da burin yi wa mutum kashi 40% allurar rigakafin cutar a kasar nan na da karshen shekara sannan ta yi wa mutum kashi 70% rigakafin a shekara mai zuwa.

Share.

game da Author