Korona ta kashe mutum 6,400 cikin mako daya a Afrika – WHO

0

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa mutum 6,400 sun mutu a cikin mako daya a Afrika.

Kakakin shugaban majalisar Dinkin Duniya UN Antonio Guterres, Stéphane Dujarric ya fadi haka a taron da ya yi da manema labarai a hedikwatar UN dake New York a cikin wannan mako.

Stéphane ya ce wannan shine karon farko da cutar ke kisan mutane da yawa a Nahiyar Afrika.

Ya ce kasashen Afrika ta Kudu da Tunisia na da kashi sama da 55% daga yawan mutanen da cutar ta kashe a Afrika.

Cutar korona ta sake barkewa a Afrika karo na uku yayin da yankin ke kokarin kara yawan maganin allurar rigakafin domin dakile yaduwar cutar.

Yankin na jiran ta karbi kwalaben maganin rigakafin har miliyan 12 dake hanya.

Afrika na bukatar kwalaben maganin rigakafin har miliyan 183 domin yi wa mutum kashi 10% rigakafin Nan da watan Satumba.

Sannan yankin za ta bukaci miliyan 729 na maganin rigakafin domin yi wa mutum kashi 30% a karshen shekaran nan.

Najeriya

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa mutum 29 ne suka mutu a dalilin kamuwa da cutar korona daga ranar Litini zuwa Alhamis a Najeriya.

Hukumar ta ce Najeriya ta samu wannan karuwa bayan mutum 11 din da suka mutu bayan kamuwa da cutar ranar Alhamis.

A wannan rana mutum 566 sun kamu a jihohi 11 da Abuja.

Mutum 283 sun kamu a jihar Legas, Akwa-ibom-88, Oyo-62, Rivers 62, Abuja-18, Ogun-12, Kwara-11, Filato-6, Zamfara-3, Kaduna-2 da Katsina-2
Mutum 176,577 sun kamu sannan an sallami mutum 165,323 daga cikin su.

Mutum 9,066 na killace a dalilin kamuwa da cutar sannan mutum 2,178 sun mutu.

Cutar korona ta sake barkewa karo na uku ranar da kungiyar likitoci na NARD suka fara yajin aiki.

Zuwa yanzu yajin aikin da likitocin suka fara ya Kai kwanaki hudu kenan ba tare da alamun ko za su dakatar da yakin aikin.

Share.

game da Author