Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa an samu karin mutum 790 da suka kamu da cutar korona ranar Laraba.
An gano wadannan mutane a jihohi 12 da Abuja.
Alkaluman da aka fitar ranar Laraba sun nuna cewa mutum 574 sun kamu a jihar Legasz Rivers-83, Ondo-38, Ogun-31, Oyo-23, Delta-10, Abuja-9, Ekiti-7, Edo-6, Osun-4, Anambra-2, Bayelsa-2 da Filato-1.
NCDC ta ce cutar ta fi yaduwa neca jihohin Legas, Akwa-Ibom, Rivers , Oyo da Abuja.
Gwamnati ta yi kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar domin kare kansu da na kusa da su daga kamuwa da cutar.
Hukumar NCDC ta ce mutum daya ya mutu ranar Laraba inda hakan ya kawo jimlar adadin yawan mutanen da suka mutu a dalilin cutar zuwa 2,195
Mutum 166,203 sun warke sannan mutum 11,500 na killace a asibiti.
Idan ba a manta ba kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa mutum 6,400 sun mutu a cikin mako daya a Afrika.
Kakakin shugaban majalisar Dinkin Duniya UN Antonio Guterres, Stéphane Dujarric ya ce wannan shine karon farko da cutar ke kisan mutane da yawa a Nahiyar Afrika.
Ya ce kasashen Afrika ta Kudu da Tunisia na da kashi sama da 55% daga yawan mutanen da cutar ta kashe a Afrika.
Cutar korona ta sake barkewa a Afrika karo na uku yayin da yankin ke kokarin kara yawan maganin allurar rigakafin domin dakile yaduwar cutar.
Yankin na jiran ta karbi kwalaben maganin rigakafin har miliyan 12 dake hanya.
Discussion about this post