A ci gaba da yaɗuwa da kisan mutane da Korona mai saurin kisa ke yi, mutum biyar suka yi sallama da duniya a sanadiyyar kamuwa da ita ranar Litinin.
Hukumar Dakile yaɗuwar cututtuka, NCDC, ta sanar cewa mutum biyar sun mutu ranar Litinin kuma mutane sama da 400 sun kamu da Korona a wannan rana.
Korona ta kwashi mutum 190 a jihar Legas wanda aka tabbatar sun kamu da ita, sai kuma jihar Ribas da mutum 86 suka kamu.
Jihar Ogun na da mutum 85 sabbin waɗanda suka kamu, Oyo mutum 22,Abuja mutum 29, Kwara mutum 7 sai kuma Edo, mutum 5.
Jihar Abiya na da mutum 4 sai Bayelsa dake da mutum 3 sabbin waɗanda suka kamu.
Zuwa yanzu sama da mutum 9,000 ne ke ɗauke da korona a kasarnan sannan mutum miliyan 2.5 aka yi wa gwajin cutar a kasar.
Discussion about this post