Hukumar Dakile yaɗuwar cututtuka NCDC, ta sanar cewa mutum 2 sun mutu ranar Talata kuma mutane sama da 610 sun kamu da Korona a wannan rana.
Korona dai na ci gaba da yaduwa da kisar mutane a kasar nan a dalilin bullowar Korona mai saurin kisa wato Delta.
Mutum 281 a jihar Legas, Rivers-152, Akwa-ibom-85, Ogun-21, Oyo-21, Ekiti-14, Abuja-13, Bayelsa-2 da Kano-2.
Zuwa yanzu mutum 166,131 sun warke daga cikin mutum 179,118 da suka kamu a kasar nan.
Mutum 2,194 sun mutu sannan mutum sama da 10,000 na dauke da cutar a Najeriya.
An yi wa mutum miliyan 2.5 gwajin cutar a kasar.
Gwamnati ta yi kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar domin samun kariya daga kamuwa da cutar.
Idan ba a manta ba a ranar Lahadi ne kwamitin PSC ta sanar cewa gwamnati ta dage ranar yi wa mutane allurar rigakafin cutar korona zango ta biyu.
Bisa ga takardar sanarwar wanda darektan yaɗa labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya Willie Bassey ya saka wa hannu Boss Mustapha ya ce gwamnati ta yanke wannan hukunci ne saboda wasu matsaloli da suka sha mata kai.
Kafin wannan lokaci dama kuma gwamnati ta sanar da ranar Talata 10 ga Agusta ranar da za a fara yi wa mutane allurar rigakafin zango ta biyu a asibitin FMC dake Jabi a Abuja.
Sai dai a safiyan Litini gwamnati ta sake fitar da sanarwar cewa za a fara yi wa mutane rigakafin Korona zango na biyu ranar 16 ga Agusta.
Shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ta ƙasa NPHCDA Faisal Shu’aib ya sanar da haka.
Shu’aib ya ce gwamnati ta dage ranar yin allurar rigakafin zango na biyu domin hukumar NPHCDA ta samu lokacin yin shirye-shiryen da ya kamata.
Discussion about this post