Ga dukan alamu yaduwar cutar korona ya wuce yadda ake tsammani a Kasar nan yanzu inda tsakanin ranakun Alhamis da Juma’a cutar ta yi ajalin mutum 11 a kasar nan.
Korona ta yi ajalin mutum 7 a ranar Laraba sannan mutum 8 ranar Alhamis, ranar Juma’a kuma mutum 3.
Kisar mutum 11 da korona ta yi ya kawo yawan waɗanda cutar ta kashe a ƙasar nan zuwa mutum 2,247.
Hukumar NCDC ta ce mutum 674 ne suka kamu da cutar ranar Alhamis sannan a ranar wannan Juma’a mutum 304.
A ranar Laraba mutum 1,149 suka kamu da cutar a kasar nan.
NCDC ta danganta yawaitar fantsamar cutar da rashin yi wa jama’a masu yawa allurar rigakafin korona.
Zuwa yanzu mutum 185,571 ne suka kamu, an sallami mutum 168,124 a kasar nan.
Idan ba a manta ba a ranar Litini da ya gabata ne gwamnati ta fara yi wa mutane allurar rigakafin korona zango na biyu da maganin rigakafin na ‘Moderna’ wanda kasar Amurka ta bai wa kasar nan kyauta.
Bayan haka gwamnati ta kuma karbi kwalaben maganin rigakafin na Johnson & Johnson guda 177,600 daga hannun AU.
Daga nan gwamnati ta karbi kwalaben maganin rigakafin na Oxford-astraZeneca guda 699,760.
Gwamnati ta ce za ta yi amfani da maganin Oxford-astraZeneca da ta karba domin karike yi wa mutanen da suka yi allurar rigakafin da ruwan maganin a zango na farko.
Gwamnati ta yi kira ga mutane musamman wadanda suka dara shekaru 18 da su yi allurar rigakafin domin samun kariya daga cutar.
Sannan ta kara yin kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar domin kare kansu da na kusa da su daga kamuwa da cutar.