Shugaba Muhammadu Buhari zai killace kan sa bayan dawowar sa daga Landan, kamar yadda dokar Hukumar Daƙile Yaɗuwar Korona ta Ƙasa (NCDC) ta tanadar.
Haka su ma sauran ‘yan tawagar da su ka raka shi Landan ɗin inda su ka shafe tsawon makonni biyu, su ma duk za su killace kan su.
Waɗanda su ka dafa masa baya a tafiyar sun haɗa da Ministan Harkokin Waje, Jeoffrey Onyeama; Ƙaramin Ministan Ilmi, Chukwemeka Nwajuiba; Mashawarci Kan Tsaro, Babagana Monguno da Babban Daraktan Leƙen Asiri, Ahmed Abubakar.
Buhari da ‘yan rakiyar sa sun tafi Landan tun a ranar 26 Ga Yuli, bai dawo ba sai a ranar Juma’a, bayan ya shafe sati biyu.
Kakakin Yaɗa Labarai na Shugaba Buhari, Garba Shehu ya ce Buhari da jami’an za su killace kan su kamar yadda doka da tsarin tafiye-tafiye na duniya ya gindaya.
“Shugaba Buhari da dukkan ‘yan tawagar sa za su killace kan su. Bayan sun iso Najeriya an yi masu gwaji a ranar Juma’a ɗin, kuma nan gaba kaɗan za a ƙara yi masu wani gwajin.” Inji Garba Shehu.
A lokacin da ya ke Landan, Buhari ya shiga sahun wasu shugabannin duniya inda aka yi Taron Makomar Ilmi a Duniya.
Buhari ya tafi Landan ganin likitocin sa, kwanaki kaɗan kuma likitocin Najeriya su ka tsunduma yajin aikin da har yau ba su koma ba.
A Landan, Buhari ya kai wa jagoran APC, Bola Tinubu ziyara, wanda shi ma neman magani ya kai shi Landan ɗin.
Discussion about this post