Korona bata ɗaga wa ƴan Najeriya ƙafa ba ranar Juma’a mutum 10 ta yi ajalin rayukansu cikin har da tsohon sanata

0

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa mutum 618 sun kamu da cutar korona kuma wasu mutum 10 sun mutu ranar Juma’a a Najeriya.

NCDC ta ce an gano wadannan mutane a jihohi 14 da Abuja.

Zuwa yanzu mutum 190,333 ne suka kamu da cutar a Najeriya sannan mutum 2,308 sun mutu.

An sallami mutum 180,210 cikin wannan adadi amma kuma mutum 17,791 na ɗauke da cutar.

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Legas Akin Abayomi ya bayyana cewa cutar korona ta yi ajalin mutum 10 tsakanin ranar 24 zuwa 25 a jihar.

Abayomi ya ce daga cikin mutum 10 din da suka mutu a jihar akwai tsohon sanata Biyi Durojaiye wanda ya rasu ya na da shekaru 88 da shugaban jami’iyyar PDP reshen jihar Legas Dominic Adegbola wanda ya rasu shima yana da shekaru 73 a duniya.

Ya ce a ranar 25 ga Agusta ne gwamnati ta fara yi wa mutane allurar rigakafin korona a wurare 183 a jihar.

Abayomi ya yi kira ga wadanda basu yi rigakafin ba da su hanzarta zuwa yin allurar domin samun kariya.

Sai dai mutane da dama sun ce ba su iya yin allurar rigakafin cutar bane saboda rurrufe wuraren da aka bude domin yin allurar rigakafi.

Zuwa yanzu gwamnati ta yi wa mutum 3,966,005 allurar rigakafin korona a kasar nan inda daga ciki mutum sama da miliyan biyu sun yi allurar rigakafin zango na biyu.

Share.

game da Author