KORONA: Ba za a saka dokar Kulle a Najeriya duk ƙarin yaɗuwar Korona da ake samu

0

Gwamnati Najeriya ta bayyana cewa babu wani shori da gwamnatin ke yi na sake saka zaman gida dole duk da karuwar yawan waɗanda ke kamuwa da Korona da ake yi.

A ranar Alhamis ne gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ba ta da niyyar saka dokar zaman gida dole duk da samun karuwa a yaduwar cutar korona da ake sanu a kasar nan.

Ministan lafiya Osagie Ehanire ya ce gwamnati za ta saka dokar ne idan tura ta kai bango.

“A lokacin da gwamnati ta saka dokar zaman gida dole mutane, masana’antu, gwamnati da tattalin arzikin kasar nan sun tsaya cak duk da cewa gwamnati ta tallafawa wa mutane da abinci da kudade domin rage raɗaɗin kunci zaman gida.

Zuwa yanzu cutar ta sake barkewa karo na uku a kasar nan inda a dalilin haka ya sa ake samun karuwa a yaduwar cutar.

Bisa ga alkaluman da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta fidda ranar Laraba, Najeriya ta samu mutum 790 da suka kamu da korona.

A jimla Najeriya ta samu sama da mutum 179,000 da suka kamu da cutar sannan mutum 2,195 sun mutu
Tun lokacin da aka gano nau’in cutar mai saurin yaduwa wato ‘Delta’ aka fara samun karuwa a yaduwar cutar.

Mutum 11,500 ne dauke da cutar a kasar nan.
Jami’an lafiya da hukumomin lafiya sun gargadi ‘yan Najeriya da su rika kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar domin samar wa kansu da na kusa da su kariya daga kamuwa da cutar.

Share.

game da Author