Gwamnnan jihar Katsina, Aminu Masari ya bayyana cewa gwamnatin sa ba za ta zuba ido jami’an hukumar kwastan na kashe mutanen da basu ji ba ba su gani ba a jihar da sunan wai suna farautar ƴan sumogal.
Masari ya ce gwamnati na nazarin maka hukumar kwastan ɗin a kotu bisa wannan mummunar abu da suka yi.
” Wannan ba shi ne karon farko da jami’an kwastan ke kashe mutanen jihar mu ba. Idan muka maka su a kotu zai zama ishara ga sauran jami’an nan gaba.
Masari ya ce gwamnati ba za ta sake ɗaukar irin haka ba.
Idan ba’a manta ba, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda jami’an Kwastan suka kashe wasu mutane biyar a lokacin da suke kokarin kama wasu da suke zaton sun yo fasakwaurin buhunan shinkafa ne.
A dalilin haka mazauna garin jibiya sun babbake motan kwastan din.
Discussion about this post