KISAN MATAFIYA A JOS: Buhari zai gana da Ɗahiru Bauchi, ya wakilta Minista Pantami ya je masa ta’aziyya

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya wakilta Ministan Sadarwa Isa Pantami ya jagoranci zuwa ta’aziyya ga Sheikh Dahiru Bauchi bisa ga kisan gilla da aka yi wa ɗaliban sa.

Buhari ya aika tawagar yin ta’aziyya da jajen, kwana ɗaya bayan ya umarci jami’an tsaro su tabbatar sun kamo waɗanda su ka yi kisan.

Tuni dai Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Filato ta bayyana kama mutum 20, tare da ceto wasu mutum 33.

Wata sanarwar da aka buga a shafin Facebook na Minista Pantami a ranar Lininin, ta nuna tuni Pantami ya isa gidan Shehun Malamin a Bauchi, domin an nuna hoton su a tare su na gaisawa.

Sannan kuma ya isa da muhimmin saƙon cewa an tabbatar masa da Gwamnati ta bada umurni a binciki masu laifi, a yi musu hukunci kamar yadda doka ta tsara.

Idan ba a manta ba, an nuno Ɗahiru Bauchi a kafafen yaɗa labarai da bidiyo tun a ranar Lahadi ya na bayanin cewa kada a ɗauki fansa, a jira a ga abin da gwamnati za ta iya yi.

“Idan kuma gwamnati ba za ta iya hukunta masu kashe mu ba, kuma ba za ta iya kare mu ba, to ta sauka ta bari waɗanda za su iya su hau mulkin.”

Ɗahiru Bauchi ya ƙara da cewa daga yanzu ba za mu ƙara yarda ba.

Pantami ya gana Ɗahiru Bauchi, sannan ya isar da ta’aziyya kuma Shugaban Ƙasa zai gana da malamin bayan bayan ya kammala kwanakin zaman killace kan sa da ya ke yi, sakamakon dawowar da ya yi daga zaman makonni biyu a Landan, domin duba lafiyar sa.

Minsita Pantami ya kuma isar da saƙon Shugaba Muhammadu na jinjina masa ganin yadda ya yi kira ga magoya bayan sa cewa aka su ɗauki ramuwar gayyar kisan da aka yi wa mabiyan malamin su 22 da kuma ji wa da dama raunuka.

Ɗahiru Bauchi shi ne malamin da ya fi kowane malami yawan mabiya a Najeriya.

Share.

game da Author