Akalla fasinjoji 5 ne rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta tabbatar sun halaka a hadarin jirgin ruwa da ya kife a cikin ruwa a kauyen Mareniyo dake Karamar Hukumar Ardo-Kola.
Wani mamban cocin ‘Christian Reformed Church in Nations (CRCN)’ ya ce a cikin wadanda suka mutu harda faston cocin mai suna Shedrack Bako.
Hatsarin ya auku ne a lokacin da jirgin ruwan dake dauke da fasinjoji 14 da kaya ya biyo ruwa daga Mareniyo zuwa wani kauye dake karamar hukumar Karim Lamido ranar Talata.
Majiya ya ce ga dukan alamu jirgin ta kife ne a dalilin ambaliyar ruwa a wannan kogi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Abdullahi Usman Shima ya tabbatar da wannan hadari.
Usman ya ce an ceto mutum 9 daga cikin fasinjoji 14 dake cikin jirgin ruwan sai dai har yanzu ba a gano wasu mutum biyar ba wanda ake zaton sun mutu.
Ya ce rundunar tare da masu nutso da masunta na ci gaba da neman gawarwakin wadanda suka bace a cikin ruwan.