Yanzu dai satar shanu a ƙauyukan jihar Katsina ya zama abinda mazauna ƙauyuka jihar Katsina suka saba dashi, saboda abu ne wanda kusan a kullum sai an yi shi, jama’a ma sun saba, yanzu sabon abinda mazauna karkara ke yi shine arcewa daga garuruwar su idan yamma ta yi su komo da safiya domin ci gaba da kasuwancin su, masu zuwa gonaki su kuma su tafi gona.
Duka da cewa maharan ba da dare kawai suke sace mutane ba, ƴan gari sun ce idan suka shigo gari da dare ba sace mutane kawai da dabbobi suke yi ba, abinda ya sa suke arcewa kenan su koma manyan garuruwan da ke kusa da su, idan safiya ta yi sai su komo gidajen su.
A ƙauyukan Wurma, Batsari da Tsauwa, mutane sun bada labarin yadda suka faɗa cikin mummunar yanayi a dalilin hare-haren ƴan bindiga da suka addabe su.
Wakilin PREMIUM TIMES a hanyarsa ta zuwa Katsina daga Dutsinma tare da wasu abokan sa sun isa garin Daram da misalign karfe 7:42 na yamma. Isar su Daram ke da wuya sai suka iske gungun mata na ficewa daga wannan gari.
Sun bayyana cewa za su tsallaka garin Kurfi ne da ke da nisan kilomita 7 daga wannan gari su kwana.
Sun ce mahara za su kawo hari garin a wannan dare shine ya sa za su fice, wato su yi ƙaura zuwa Kurfi sai da safe su dawo.
Kowa ya gudu, in ji wata dattijiya mai suna Turai, “ Mazajen mu duk sun shiga daji su ɗaɗɗare bisa itatuwa, nan za u kwana, mu kuma sun ce mu tsallaka zuwa garin Kurfi mu kwana. Dukkan mu za mu tafi garin Kurfi ne mu kwana sai kuma mun ji sako daga wurin su.
“ Garuruwan mu sun fara zama Kufayi yanzu mutane sun waste saboda ƴan bindiga, Inji Nasiba, ɗaya daga cikin matan dake hijira daga Daram zuwa Kurfi.” A jiya ma sai da suka kai hari garin Sauyawa, suka sace shanu masu yawan gaske. Sai bayan sun yi tafiyarsu kafin ƴan sanda suka iso garin.
Ita ko Assibi cewa ta yi mata suna kaura zuwa garin Kurfi su kuma maza a cikin daji za su kwana.
“ Sun kai hari ƙauyukan dake makwabtaka da mu, Sauyawa, Tamu sannan suka afka kauyen Yar Randa sau uku a jere da dare. Mazajen mu sun ce abinda ya hana su ƙarisowa Daram shine ruwan sama da aka yi mai yawan gaske da ya hansu iya tsallake rafi da baburan su dake tsakanin mu da ƙauyukan.
Mutanen Daram makiyaya ne, suna da dabbobi masu yawa, kuma manoman gaske ne, akwai su da rumbunan abinci masu yawa sannan kuma akwai ‘yan kasuwa masu yawan gaske. Hakan ya sa ƴan bindiga ke harin garin ba tun yanzu ba.
Aasibi ta ce mazajen su da ‘ya’yan su duk za su kwana saman itatuwa ne zuwa safe.
Da wakilin mu ya nemi ji ta bakin mahukunta, mai ba gwamnan jihar shawara kan harkar tsaro a jihar, Ibrahim Katsina ya bayyana cewa gwamnati na sane da matsalolin tsaro da ake fama da shi a jihar kuma nan ba da dadewa za a ga canji fiye da wanda yake a yanzu.
Discussion about this post