Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da cewa cutar kwalara ta kashe mutum 60 tare da kwantar da waɗansu mutum 1400 a jihar.
Kwamishinan Lafiya na Katsina, Yakubu Ɗanja ne ya bayyana haka a lokacin da yake wa Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA), ƙarin bayani a ranar Asabar.
Ya ce baya ga kisan mutum 60 da cutar amai da gudawa ta yi, wasu mutane har 1400 sun kamu da cutar ya zuwa yanzu.
Sai dai kuma Ɗanja ya ce Gwamnatin Katsina ta tashi tsaye wajen ƙoƙarin daƙile bazuwar cutar.
“Ana ci gaba da sayo magungunan cutar kwalara domin bayarwa kyauta a asibitoci. Sannan kuma jami’an lafiya na ci gaba da wayar wa jama’a kai a faɗin jihar.”
Kwamishinan ya kuma yi kira da gargaɗi ga jama’a da kiyaye ɗauka da bin matakan tsaftace abinci da muhalli da ruwan sha.
“Amai da gudawa cututtaka ne da za a iya kauce wa kamuwa da su. A kula da ɗaukar matakan tsafta, amfani da ruwa mai tsafta shi ne hanya garanti ta kauce wa kamuwa da cutar.” Inji Ɗanja.
Cutar kwalara sai fantsama ta ke yi a Arewa maso Yamma. Cikin makon da ya gabata ta ɓarke a jihohin Zamfara, Kano, Sokoto da Jigawa, kuma ta yi kisa sosai.
A jihar Kano da Jigawa kaɗai ta kashe mutum 295.
Discussion about this post