KATAFILA SARKIN AIKI: El-Rufai da Kamfanin Konexa sun fara aiki samar wa kauyukan Kaduna wutar Sola gadan-gadan

0

A ci gaba da bunkasa jihar Kaduna da gwamnatin jihar Kaduna ƙarkashin gwamna Nasir El-Rufai, a wannan karon wadata ƙauyukan Jihar shine ya ke yi.

Idan ka daɗe baka ziyarci jihar Kaduna ba musamman cikin garin Kaduna, za ka wasu irin ayyukan raya gari da baka taba gani a tsawon zaman ka a jihar.

Ayyuka gwamnati ke yi babu ƙaƙƙautawa a duk faɗin jihar.

Gwamnatin El-Rufai tare da haɗin gwiwar kamfanin Konexa za su samar wa mutanen kauyukan Kaduna da wutar lantarki ta hqnyar hasken rana, wato Sola.

Tuni har an kammala na Kauyukan Ruhugi, Chikaji,dake karamar hukumar Igabi, Jihar Kaduna.

Wannan aiki na samar da wuta zai karaɗe ƙauyukan jihar gaba ɗaya, makarantu, asibitoci da cibiyoyin kowon lafiya a faɗin jihar.

A dalilin wannan ƙokari na gwamnatin Kaduna, zuwa yanzu gwamnati ta samu rarar sama da naira miliyan 400 wanda da za a biya su ga hukumar bada wutar lantarki ta kasa ne.

Yanzu an ƙayata wurare da dama a fadin jihar da wutar lantarki na Solar, gari yayi haske.

Bayan haka wanda aka aka kaddamar a Ruhugi da cikaji zai amfanar da mutane sama da mutum 1000. Yanzu suma za su mori wuta kamar a GRA.

Mutanen gari na ci gaba da ya yabawa gwamnatin El-Rufai saboda ayyukan ci gaba da yake bijirowa da su a jihar domin talakawa, wanda ba a taɓa tunanin za a samu irin su nan kusa a jihar ba.

Share.

game da Author