Gwamnatin Tarayya ta ƙudiri aniyar tara naira tiriliyan 10.1 na kuɗaɗen harajin cikin gida a cikin 2022.
Shugaban Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa (FIRS), Mohammed Nami ne ya bayyana haka.
Nami ya yi wannan alwashin a ranar Laraba, lokacin da ya bayyana a gaban Kwamitin Harkokin Kuɗaɗe na Majalisar Tarayya, a Abuja.
Ya ce hukumar sa tuni ta tsara wani tsarin da zai tabbatar an tara waɗannan maƙudan kuɗaɗen cikin 2022.
Nami ya ce za a tara kuɗaɗen ne daga kuɗaɗen harajin da Najeriya ke samu baki ɗaya.
Da ya ke na sa jawabi, Shugaban Kwamitin Harkokin Kuɗaɗe a Majalisar Tarayya, James Dake, ya jinjina wa Shugaban Hukumar FIRS ɗin, kuma ya ƙara masa ƙwarin guiwar ganin cewa an samu waɗannan maƙudan kuɗaɗen da hukumar ta sha alwashin ta tara a cikin shekara mai zuwa.
Cikin makon jiya PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda Gwamnatin Tarayya ta tara Naira biliyan 512 na VAT daga Afrilu zuwa Yuni.
Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Kasa (NBS), ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta tara harajin jiki magayi (VAT) na naira biliyan 512.25 a cikin watanni ukun Afrilu, Mayu da Yuni.
Ƙididdiga ta nuna cewa a watanni uku na farkon shekara, Janairu, Fabrairu da Maris, kuɗaɗen da aka tara ba su kai na watannin Afrilu, Mayu da Yuni ba.
A watanni ukun farkon shekara dai an tara naira biliyan 496.39.
Hukumar Ƙididdiga wadda a Turance aka sani da National Bureau of Statistics ce ta yi wannan bayani dalla-dalla, a cikin rahoton da ta fitar a ranar Talata.
Adadin ya nuna an samu ƙarin kusan kashi 56.56 a cikin shekara ɗaya.
Masana’antu ne su ka fi biyan harajin jiki magayi (VAT), inda aka karɓi har naira biliyan 44.89 a hannun su. Sai kuma ayyukan ƙwararru daban-daban da aka karɓi harajin naira biliyan 29.30 a hannun su.
Harkokin kasuwanci da cinikayya an karɓi harajin VAT na naira biliyan 21.96 a hannun su tsakanin Afrilu zuwa Yuni, 2021.
Yayin da masana’antun suturori da dangogin su kuma su ka biya naira miliyan 77.74. Su kuma masu magunguna dasabulai da kayan da su ka danganci irin su, an karɓi harajin naira miliyan 169 a hannun su.
Daga cikin naira biliyan 512.25 ɗin da aka tara daga Afrilu zuwa Mayu, 2021, naira biliyan 187.43 na kuɗaɗen duk haraji ne daga kayan cikin gida da ake sarrafawa a cikin Najeriya.
Sai kuma naira biliyan biliyan 117.13 da aka karɓa matsayin harajin VAT na kayan da ake shigowa da su daga waje, a cikin waɗancan watanni uku.