Kashi 40% na matasan Najeriya na tu’ammali da muggan ƙwayoyi -NDLEA

0

Hukumar Hana Tu’ammali da Muggan Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta nuna matuƙar dawuwar yadda ake samun yawaitar matasa masu shan muggan ƙwayoyi a Najeriya.

Cikin wata ƙididdiga da NDLEA ta fitar, ta bayyana cewa bincike ya nuna kashi 40% bisa 100% na matasan Najeriya sun zama masu amfani da muggan ƙwayoyi.

Shugabar Sashen Binciken Muggan Kwayoyi Masu Sa Maye ta NDLEA, Atinuke Adulogu ce ta bayyana wannan ƙididdiga a Taron Masu Ruwa da Tsaki na 7 da aka yi a Mazaɓar Ojo 1 da ke Legas, a ranar Alhamis.

Ta ce wannan adadi na yawan matasa masu shan muggan ƙwayoyi barazana ce babba ga ƙoƙarin da ake yi na ganin an bunƙasa ƙasar nan.

Atinuke ta ce alƙaluman abin damuwa ne sosai, domin da matasa ƙasa ke dogaro wajen ganin an cicciɓa kowane fanni an samu ci gaba.

“A gaskiya wannan adadin ƙididdiga ya nuna cewa shan muggan ƙwayoyi a Najeriya ya tashi daga matsala ya kai annoba kuma gagarima.

“Shin ya ake tunanin nan gaba ƙasa za ta kasance, idan kashi 40% bisa 100% na matasan ta na shan muggan ƙwayoyi?”

Atinuke ta ce lamarin ya na kawo tsaiko, naƙasu da barazana ga kiwon lafiyar al’umma da kuma tsaron lafiyar su.

Daga nan sai ta yi kira a haɗa hannu a taimaki Hukumar NDLEA domin a daƙile wannan mummunar ɗabi’a ta shan muggan ƙwayoyi a zukatan matasan ƙasar nan, musamman ‘yan shekaru 18 zuwa 35.

Share.

game da Author