Kwamitin Lura da Kuɗaɗen Gwamnantin Tarayya na Majalisar Tarayya ya bai wa Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa (NPA) kwanaki 14 ta fito da bayanan naira biliyan 225, waɗanda su ka shiga duhu tsakanin 2019 zuwa 2020.
Shugaban Kwamiti James Feleke ya zargi Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa da kasa bada rahoton bayanan kuɗaɗen da ta kashe da waɗanda ta samu a shekarar 2019 da kuma 2020.
A zaman Kwamitin Harkokin Kuɗaɗe a ranar Alhamis a Abuja, an umarci NPA ta samu Hukumar Kula da Kashe Kuɗaɗen Gwamnantin Tarayya (FRC) domin ta tsefe ƙididdiga dalla-dalla har a fito da bayanan kashe kuɗaɗe na 2019 da kuma 2020.
Tun da farko dai Bello Gulma, wanda shi ne Shugaban Sa-ido kan Kuɗaɗen Gwamnantin Tarayya a Hukumar FRC, ya shaida wa kwamitin cewa har yau Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa (NPA) ba ta bayar da bayanan kuɗaɗen 2019 da na 2020.
“Tun da NPA ta bayar da lissafin kuɗaɗe na 2018, har yau ba ta bayar da na 2019 da 2020 ba.” Inji Bello Gulma.
Shi kuwa wakilin da Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa (NPA) ta tura a gaban kwamitin domin ya wakilce ta, Emeka Ezengwu, ya bayyana cewa ba a daɗe ba da Hukumar Gudanarwar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta sa wa rahoton 2019 hannu. Shi kuma rahoton binciken kuɗaɗen na 2020, har yanzu ana aiki a kan sa.
Discussion about this post