Karamar Hukuma a Kano ta haramta hirar dare tsakanin ‘yan mata da samari

0

Karamar hukumar Rano ta soke zancen dare tsakanin masu neman aure a fadin yankin karamar hukumar.

Shugaban karamar hukumar Dahiru Muhammed me ya sanar da hakan bayan kammala taron kwamatin tsaro na karamar hukumar a ranar laraba.

Alhaji Muhammed Wanda shine shugaban kwamatin yace an dauki wanna mataki ne domin kawo tsafta tsakanin masu neman aure wadanda suke zance da daddare.

Shugaban karamar hukumar ya umarci jami’an Hisba da ‘yan sanda da sarakuna su tabbatar da ganin ana bin umarnin.

A nasa jawabin Hakimin Rano, Wamban Rano Alhaji Mannir Tafida Abubakar ya bukaci Dagatai da Limamai du bada hadin Kai da goyon baya domin samun nasarar sabuwar dokar.

Wamban Rano yace abubuwa marasa dadi suna faruwa tsakanin ‘yan mata da samari lokacin da suke zancen dare, hakan me yasa karamar Hukumar daukar matakin domin kawu gyara.

Hakimin yace yakamata iyaye su kula da ‘ya’yansu kuma su baiwa dokar goyon baya, kuma duk iyayen da sukayi sake wani abu ya kuma faruwa, su za’a daurawa laifi.

Share.

game da Author