Kamfanin Mai na Kasa, NNPC ta sanar da sabbin sauye-sauye a kamfanin.
Kamfanin Mai din ta sauya wa wasu manyan manajoji da darektocin kamfanin wuraren aiki.
Daya daga cikin canjin da aka yi shine maida fitaccen ɗan jarida Garba Mohammed babban manaja a sashen hulda da jama’a, GPAD.
Sauran sun haɗa da
Aisha Ahmadu-Katagum
Adeyemi Adetunji
Mohammed Abdulkabir Ahmed
Shugaban kamfanin Mai ta na ƙasa, Mele Kyari ya ce ma’aikatar ta yi wannan canje-canje ne domin a samu ci gaba a ayyikan da aka saka a gaba don a samu nasara a kamfanin.