Babbar Kotun Birnin Kebbi ta maida Shugaban Jam’iyyar PDP, Uche Secondus a kan kujerar sa a ranar Alhamis.
Kotun ta maida shi ne kwanaki uku bayan Babbar Kotun Fatakwal a Jihar Ribas ta dakatar da shi, a wata ƙara da aka maka shi a ranar Litinin.
Wasu mutane biyu mambobin jam’iyyar PDP uku da su ka haɗa da Yahaya Usman, Abubakar Muhammad da kuma Bashar Suleman ne su ka shigar da ƙarar a Babban Kotun Kebbi, a ranar 25 Ga Agusta, 2021, su ka nemi a soke dakatarwar da Babbar Kotun Fatakwal ta yi wa Secondus.
Lauyan mutanen uku mai suna Ibrahim Jibril, ya riƙa kotun ta dubi ƙarar da su ka shigar, a maida Uche Secondus kan shugabancin PDP.
Mai Shari’a Nusirat Umar ta amince kuma ta maida shi, bisa hujjoji da dalilan da ta bayar. Ta ce ya ci gaba da kasancewa kan muƙamin sa har sai hukuncin da kotu ta zartas kan sa tukunna.
Wasu Gwamnonin PDP ne da mambobin jam’iyyar su ka kitsa tuggun cire shi, bisa zargin shugabancin sa ya kawo rigima a cikin jam’iyya, har wasu gwamnoni, sanatoci da manyan ‘yan jam’iyya na komawa jam’iyyar APC.
Hukuncin da Kotun Kebbi ta yanke na kuma nuna cewa Sanata Nazifi Suleiman da ya kira kan sa shugaban riƙo, shi ma an haramta shugabancin sa na riƙo kenan.
Premium Times ta buga labarin yadda lemar PDP ta kama wuta, har wani mai iƙirarin shugabancin jam’iyya ya kafa ta shi lemar jefe ɗaya.
Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Arewa, Suleiman Nazifi ya bayyana kan sa a matsayin shugaban riƙon jam’iyyar PDP, lamarin da ya ƙara hargitsawa da dagula matsalolin da suka dabaibaye jam’iyyar a ƙasa baki ɗaya.
Iƙirarin sa ya biyo bayan hukuncin da Babbar Kotun Jihar Ribas ta yanke, inda ta umarci Shugaban PDP na Ƙasa, Uche Secondus ya daina kiran kan sa shugaban jam’iyya na ƙasa.
Nazifi, wanda tsohon sanata ne daga Jihar Bauchi, ya bayyana kan sa a matsayin shugaban PDP na ƙasa na riƙo, a hedikwatar PDP ta ƙasa da ke Abuja, bayan Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Kudu, Yemi Akinwonmi shi ma ya bayyana kan sa a matsayin shugaban riƙo.
A ranar Litinin ce dai Babbar Kotun Jihar Ribas ta umarci Secondus ya daina kiran kan sa shugaban jam’iyya, kuma ya daina shiga duk wasu harkokin jam’iyya, har sai ranar da kotu ta tsaida hukuncin da ta yanke a kan sa.
Bayyana wannan hukunci ke da wuya, sai Akinwonmi, Mataimakin Shugaba na Shiyyar Kudu, ya yi amfani da Sashe na 45 (2) na dokokin PDP, ya bayyana kan sa a matsayin shugaban riƙo, kafin kotu ta tsaida hukuncin da ta yi wa Secondus.
Dokar PDP dai ta nuna cewa Akinwonmi ne zai zama shugaba tunda daga kudu ya fito, idan babu Secondus, ki kuma aka cire shi.
Sai dai shi kuma Sanata Nazifi ya yi amfani da Dokar PDP sashe na 47 (4) ya naɗa kan sa shugaban riƙo. Kuma ya kira taron Shugabannin Zartaswa na PDP, inda mutum 8 daga cikin 18 su ka halarta.
Makonni biyu da su ka gabata, wannan jarida ta buga labarin da Secondus ya ce ba zai sauka daga shugabancin PDP ba, sai ranar da wa’adin sa ya cika.
Haka kuma mun buga labarin da Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewa ba shi ya cinna wa lemar PDP wuta ba.
Shugaban Jam’iyyar PDP mai fuskantar matsin-lamba, Uche Secondus, ya bayyana cewa ba zai sauka daga shugabancin PDP ba, tunda bai aikata laifin komai ba.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Secondus, mai suna Ike Abonyi ya fitar, ta ce duk wani mai tayar da jijiyar wuyar neman Secondus ya sauka, to ya fara fitowa da laifukan da ya yi kowa ya gani tukunna.
Sanarwar ta ce bai aikata wani laifin da za a ce ya cancanci saukewa ko wajibcin saukewa ba.
“Saboda haka wasu ‘yan tsirarun da ke cewa Secondus ya sauka, su fito su bayyana laifukan da ya aikata.
“Secondus ba zai suka ba, zai ci gaba da jagorantar PDP tare da yi mata kyakkyawan riƙon da ya yi rantsuwar zai ci gaba da yi mata, watanni 44 da su ka gabata da aka rantsar da shi.”
Wannan kakkausan jawabi yazo ne sa’o’i kaɗan bayan Mambobin Majalisar Tarayya na PDP sun nemi Secondus ya sauka daga shugabancin jam’iyyar.
Sun ce akwai hatsari nan gaba idan Secondus ya ci gaba da kasancewa shugaban PDP.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda lemar PDP ta kama da wuta, bayan wasu jiga-jigan jam’iyya takwas sun yi murabus, sun bar gwamnonin su da kururuwar neman gudummawar kashe gobara.
Kwana ɗaya bayan jiga-jigan jam’iyyar PDP su bakwai sun ajiye ayyukan su na shugabancin jam’iyya a matakai daban-daban na ƙasa, an samu tsohuwar Sanata Joy Emordi, ɗaya daga cikin Shugabannin Kwamitin Amintattun PDP ta koma jam’iyyar APC.
Sai dai kuma duk da wannan koma baya da PDP ta samu,gwamnonin jam’iyyar sun roƙi a kwantar da hankali kuma a kai zuciya nesa, za su kyara wa gobarar ruwa su kashe wutar.
Gwamnan Sokoto kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin PDP, Aminu Tambuwal ne ya yi kiran a Abuja.
Yayin da ya ke jaddada cewa za su shawo kan lamarin, Tambuwal ya ce PDP ce jam’iyyar da ƙasar nan ta zura wa ido tare da fatan za ta saisaita damalmalawar da mulkin APC ya yi wa Najeriya.
Waɗanda Su Ka Ajiye Muƙaman Su:
Masu riƙe da muƙamin mataimaka a muƙamai bakwai ne su ka ajiye aikin su a ranar Talata, daga Babban Kwamitin Zartaswar PDP.
Akwai Mataimakin Sakataren Yaɗa Labaran PDP na Ƙasa, Diran Odeyemi; Mataimakin Mashawarci a Fannin Shari’a, Ahmed Bello; Mataimakiyar Shugabar Mata, Hadizat Umoru da kuma Mataimakiyar Mai Binciken Kuɗi, Divine Amina Arong.
Sai kuma Mataimakin Sakataren Tsare-tsare, Hassan Yakubu; Mataimakin Sakataren Kuɗi, Irona Alphonsus.
Dukkan su sun ce sun sauka ne saboda zargin su cewa Shugaban Jam’iyya Uche Secondus bai iya tafiyar da shugabancin jam’iyyar bisa yadda ya dace ba.
Ba Ni Na Cinna Wa Lemar PDP Wuta Ba -Atiku
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya yi watsi da surutan bayan fage da ake yi cewa shi ne ya ruruta wutar rikicin jam’iyyar PDP wanda ke neman zama gobarar jam’iyya a yanzu.
Atiku na ɗaya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP da ake nunawa da yatsa cewa su na ƙoƙarin tumɓuke Shugaban PDP na Ƙasa, Uche Secondus.
Atiku ya bayyana cewa shi ƙoƙarin tabbatar da haɗin kai da kuma ɗinke ɓaraka ya yi a cikin PDP, maimakon ruruta wutar rikicin da wasu ke cewa ya yi.
Ya ce ya goyi bayan sasantawa da kuma haɗin kan jam’iyyar PDP kamar yadda aka ga ya riƙa yi a baya-bayan nan.
Daga nan ya yi kira da kowa ya haƙura, a maidai takubba cikin kube, domin ci gaban PDP a ƙasa baki ɗaya.
Atiku ya ce bai kamata jam’iyyar adawa ta faɗa cikin rikici ba, a daidai lokacin da jam’iyya mai mulki ta kasa cika wa al’umma alƙawurra, kuma a lokacin da ‘yan Najeriya su ka gaji da mulkin ta.
Ya ce ya kamata a samu haɗin kai a PDP, domin a kawar da APC a zaɓen 2023.
“Duk masu son ci gaba da mulki ko da talakawan ƙasar nan ba su so ne ke ta ruruta wutar rikice-rikice a cikin PDP, don kada mulki ya suɓuce daga hannun sa idan zaɓen 2023 ya zo.”