Jami’an rundunar Sibul Difens sun kama wata babbar mota danƙare da jabun Kananzir har lita 45,000 a jihar Neja

0

Rundunar tsaro na Sibul Difens NSCDC a jihar Neja sun kama wata mota danƙare da lita 45,000 na jabun kananzir a jihar.

Hukumar ta kama motar a hanyar Neja zuwa Kaduna ranar 15 ga Agusta.

Kwamandan rundunar na jihar, Haruna Zurmi ya sanar da haka da yake zantawa da manema labarai ranar Lahadi a garin Minna babban birnin jihar Neja.

Zurmi ya ce hukumar ta kama direban da wani abokin tafiyarsa a cikin motar.

“Mun kama direbar motar mai suna Salisu Idris dake da shekaru 45 da abokin tafiyarsa Bashir Mohammed mai shekara 25. Jami’ai sun gano cewa direban da abokin tafiyar sa basu da takardun izinin daukar kananzir din da aka kama su da shi tun a farko.

Ya ce za a maka wadannan mutane kotu domin a yanke musu hukunci da zarar hukumar ta kammala bincike.

Zurmi ya yi kira ga mutane da su guji shiga sana’an siyar da jabun kananzir domin hukumar ba za ta ja da baya ba wajen ganin ta kama duk wadanda ke da hannu a siyar da jabun kalanzir a ko ina a ciki da wajen jihar.

Ya kuma yi kira ga mutane da su ci gaba da mara wa jami’an tsaro baya wajen kawar da miyagun mutane irin haka a jihar da kasar nan baki daya.

Share.

game da Author