Jami’an Hukumar Hana Sha da Safarar Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) sun damƙe wata mata ɗauke da sunƙin hodar Iblis a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Lagos.
Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama matar mai suna Edith Ebere Okafor a cikin fasinjojin da ake lodi zuwa Monrovia, babban birnin Liberia. Jirgin dai na ƙasar Cotevoire ne.
Babafemi ya ce an kama matar a ranar 31 Ga Yuli, 2021 lokacin da ake binciken kayan fasinjojin da za su hau jirgin.
Ya ce wanda ake zargin ta yi ƙunzugun sunƙin hodar 35 a cikin ɗan kamfai, da nufin ta wuce ba tare da jami’an tsaro sun tattaɓa mata abin da ke cikin wandon na ta ba.
Sai dai kuma rana ta ɓaci yayin da jami’an tsaro su ka ware ta zuwa wajen binciken ƙwaƙwaf.
Babafemi ya ce an yi mata tambayoyin da aka kai ga gane cewa ta ɓoye muggan ƙwayoyi a cikin al’aurar ta.
“Da aka tambaye ta dalilin wannan ganganci da ta yi, matar ta ce ta yi haka ne saboda masifar son kuɗancewa cikin ƙanƙanen lokaci.”
Ya ƙara da cewa an kuma kama wani fasinja namiji da ke kan hanyar sa ta zuwa Santanbul, babban birnin ƙasar Turkiyya, a ranar 27 Ga Yuli.
“An kama shi da kilogiram 78 na tabar wiwi, wadda aka haɗa da ganyen miya.
“A waccan rana ce dai aka kama wani fasinja mai suna Egbon Osarodion, wanda ke kan hanyar zuwa Italy duk a filin jirgin na Legas.
Har ila yau, Babafemi ya bayyana yadda aka jami’an NDLEA da ke Kontagora a Jihar Neja, su ka fara wani ɗajin ajiya a ƙauyen Mailefe cikin Ƙaramar Hukumar Kontagora.
Ya ce an kasa ɗakin a ranar 29 Ga Yuli, yayin da aka gano cewa ana tara ƙwayoyin da ake yi wa ‘yan bindiga safara a cikin ɗakin.
“Bayan an yi bincike a ɗakin ajiyar, an gano buhunan wiwi 125, yayin da wani mutum da aka samu ya na Sallah a ƙofar gidan ya arce a cikin daji, ko sallame sallar bai tsaya yi ba.”
Shugaban Hukumar NDLEA Buba Marwa, ya jinjina wa jami’an da su ka yi kame a filin jirgin Legas da na Kontagora.