Jami’an Kwastam sun kama shinkafa, motoci da kayan abinci da suka kai naira miliyan 60 a Katsina

0

Hukumar kwastam reshen jihar Katsina ta bayyana cewa daga ranar 8 ga Yuli zuwa 3 ga Agusta ta kama motoci 13, buhun shinkafa 314 da wasu kayan da gwamnati ta hana shigowa da su kasar nan da kudinsu ya kai miliyan 60 a jihar.

Shugaban hukumar na jihar Katsina Dalha Wada, ya sanar da haka a farkon wannan makon a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Kaduna.

Wada ya ce motocin da aka kama sun hada da mota kirar Lexus Saloon 2011 da ta kai naira miliyan 3.6, Toyota Corolla 2015 dfa ya kai naira miliyan 7, Marsandi 180 1998 da ya kai naira miliyan 1.8, Marsandi C230, 2006 da ya kai naira miliyan 2.3, Peugeot 504 guda biyu.

Hukumar ta kama mota kirar J5 Peugeot, J5, Ford van F150 199, J5 Iveco, babbar mota tifa, Toyota Rav 4, Toyota Highlander.

Hukumar ta kama buhunan shinkafa 314, jarkunan man gyada 227 da katan din taliya 178.

Hukumar ta kama buhunan dabino da ya kai na naira miliyan 2.2, buhunan waken soya, buhunan da takin zamani.

Wada ya ce hukumar ta kama baburan hawa guda 4, buhunan abincin dabbobi da jarkunan Fetur.

Share.

game da Author