INEC ta fallasa manhajar rajistar zaɓe ta bogi a yanar gizo

0

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ƴan Najeriya su yi kaffa-kaffa da wata manhajar rajistar katin shaidar zaɓe (CVR) ta yanar gizo.

Kwamishinan Zaɓe na Ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Ilmantar da masu Zaɓe, Festus Okeye ne ya bayyana haka a Abuja.

Okoye ya ce an ja hankalin INEC ga wani saƙo da ake ci gaba da watsawa ta soshiyal midiya, mai nuna wata manhajar da aka ce hukumar ta ce a ciki za a riƙa shiga ana rajistar shaidar cancanta yin zaɓe.

Okoye ya ce, “to manhajar dai ta bambanta da sahihiyar manhajar da INEC ta fitar, wadda a ciki ta amince za a riƙa yin rajista a yanar gizo.

“Sunan manhajar boge ɗin da ake yaɗawa a soshiyal midiya https://register.inec-pvc.online/.

“Saboda haka INEC na gargaɗin jama’a cewa su nesanta kan su daga wannan manhaja ta bogi, domin ba mallakar ta ba ce, ta bogi ce.” Inji sanarwar.

Ya ce INEC ba ta wakilta wata hukuma ko ƙungiya yi mata aikin yi wa ‘yan Najeriya rajistar cancantar jefa ƙuri’a ta yanar gizo ba.

“Ana sanar da jama’a cewa manhajar INEC guda ɗaya ce, kuma ita aka amince a shiga a yi rajista ta yanar gizo a cikin ta, wato https://cvr.inecnigeria.org.”

Makonni biyu da su ka gabata ne dai Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta fitar da jadawalin ranakun rajistar masu zaɓe

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana ranaku da abubuwan da za a yi dangane da rajistar masu jefa ƙuri’a da ake gudanarwa a yanzu.

Idan kun tuna, an fara aikin ne daga ranar 28 ga Yuni, 2021 kuma za a ci gaba da yin sa har zuwa ranar 11 ga Yuli, 2022.

A sanarwar da sashen yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe na hukumar ya fitar, an nuna cewa za a yi aikin a watanni uku na farko da watanni uku na biyu na wannan shekarar da mu ke ciki.

A baɗi kuma za a yi aikin a watanni uku na biyu da watanni uku na huɗu na shekarar.

Jadawalin ya nuna cewa a bana, daga 28 ga Yuni zuwa 21 ga Satumba za a gudanar da rajistar masu zaɓe.

Daga ranar 28 zuwa 30 ga Satumba kuma za a kafe sunayen waɗanda su ka yi rajista domin kowa ya duba domin tabbatar da bayanan sa da aka wallafa daidai ne ko kuma akwai gyara.

Aiki na gaba shi ne ci gaba da aikin rajistar masu zaɓe wanda za a fara a ranar 4 ga Oktoba, kuma a ci gaba da yin sa har zuwa ranar 20 ga Disamba, 2021.

A shekarar 2022 kuma, INEC za ta ci gaba da rajistar masu zaɓe a ranar 3 ga Janairu, sannan za ci gaba da yi har zuwa ranar 22 ga Maris.

Daga nan za a dakata domin kafe sunayen waɗanda su ka yi rajistar saboda su duba su tabbatar da bayanan su da aka wallafa daidai ne ko kuma akwai gyara.

Za a yi hakan ne a tsakanin ranar 26 ga Maris zuwa ranar 1 ga Afrilu, 2022.

A tsakanin ranar 11 ga Afrilu zuwa ranar 30 ga Yuni kuma za a ci gaba da gudanar da aikin rajistar masu zaɓe.

Sa’annan, kamar dai yadda aka yi a baya, za a kafe sunayen waɗanda su ka yi rajistar saboda tabbatar da ingancin su da yin gyare-gyare a inda ya dace.

Bugu da ƙari, INEC ta bayyana irin mutanen da za su iya zuwa ofishin yin rajistar.

A cewar ta, kowane ɗan Nijeriya da ya kai ɗan shekara 18 ya cancanci yin rajistar zaɓen idan har bai taɓa yin rajista a baya ba.

Haka kuma shi ma duk wanda ya taɓa rajista amma ya samu wata matsala da rajistar sa a zaɓuɓɓukan baya, wadda ya ke so a gyara masa a yanzu, shi ma zai iya zuwa.

Hukumar ta kuma ce idan mutum mai rajista ya na so a sauya masa wurin da zai kaɗa ƙuri’a zuwa wani wajen, shi ma zai iya zuwa a gyara masa.

Haka kuma duk wanda ya yi rajista amma katin sa ya ɓace ko ya lalace, shi ma zai iya zuwa a ba shi sabon katin rajistar zaɓe.

Shi ma wanda ke so a gyara masa wani bayani da aka yi masa rajista da shi a baya, kamar suna ko ranar haihuwa, to shi ma zai iya zuwa ofishin rajistar domin a gyara masa, inji hukumar.

A ƙarshe, hukumar ta bada sanarwar cewa za a ɗage aikin rajistar a Jihar Anambra a cikin Agusta 2021 saboda zaɓen gwamnan jihar da za a yi a ranar 6 ga Nuwamba, 2021.

Share.

game da Author