Hukumar tara Haraji ta Jihar Kaduna ta garkame wasu bankuna 4 saboda kin biyan tulin harajin naira miliyan N300.5

0

Hukumar tattara kudaden haraji ta jihar Kaduna (KADIRS) ta rufe wasu manyan bankuna guda hudu a garin Kaduna ranar Litinin kan kin biyan harajin naira miliyan 300.5 da ba su biya ba.

Shugaban hukumar KADIRS, Zaid Abubakar ya bayyana cewa bankunan da aka rufe sun haɗa da First Bank, Access Bank, Guaranty Trust Bank (GTB) da Bankin Sterling.

Abubakar ya shaida wa manema labarai cewa kudin na daga cikin kudaden kakkafa husumiyan su da sauran na’urorin da suka kakkafa a garin kaduna tun daga shekarar 1999 zuwa 2020 da ya kamata bankuna su biya amma suka ki.

Ya ce gwamnati na bin bankin First bank bashin harajin naira miliyan 132.6, Bankin Access Naira miliyan 84.1, GTB Naira miliyan 23.5 sai Bankin Sterling naira miliyan 60.3.

“ Mun rika aika wa bankunan tuni akai akai amma suka yi wa gwamnati kunnen uwar shegu.

“ Mun aikawa bankin sakon tuni har sau shida First Bank, mun aika wa bankin GTB, Access Bank da bankin Sterling Bank amma basu taba waiwayar mu ba.

“Kin biyan bashin harajin da gwamnati ke bin wadannan bankuna ne ya sa hukumar KADIRS ta rufe su.

“Sai dai kuma wasu daga cikin bankuna sun biya wani abu daga cikin bashin da gwamnati ke binsu sannan sun saka hannu a takardar yarjejeniyar cewa za su biya sauran kudaden nan da dan wani lokaci.

A karshe Abubakar ya yi kira shugabannin masana’antu a jihar da su rika biyan haraji ga gwamnati tunda wuri domin gujewa kada watarana hukumar ta garka me su.

Share.

game da Author