Hukumar NAFDAC ta gargaɗi mutane su daina shan maganin gargajiya bayan kwanaki 14 da haɗa shi

0

Hukumar NAFDAC ta gargaɗi mutane da su daina shan maganin gargajiya da aka hada shi bayan kwanaki 14.

Hukumar ta bada wannan gargaɗi domin kare mutane daga fadawa cikin matsaloli da ka iya cutar da lafiyar su.

Shugabar NAFDAC Mojisola Adeyeye ta fadi haka ne ranar Litini a taron ranar magungunan gargajiya ta duniya da ake yi ranar 31 ga Agusta na kowacce shekara.

Adeyeye ta shawarci ‘yan Najeriya da su rika amfani da magungunan gargajiya tare da yin taka tsantsan domin gujewa matsalolin da ka iya cutar da lafiyar su ko yin ajalin su.

Ta ce za a iya shan maganin gargajiyar da aka hada bayan kwanaki 14 idan an ajiye maganin a wurin da ke da sanyi.

“Ya zama dole mutane su rika takatsantsan wajen amfani da maganin gargajiya musamman yadda babu masaniya kan yawan maganin da ya kamata a sha.

“Ya kamata mutane su fahimci cewa maganin gargajiya ka iya zama guba sannan guba na iya cutar da mutum ko da kadan ko da yawa ne aka sha.

“Idan ka hada maganin gargajiya na ruwa sannan ya yi tsami hakan na iya cutar da lafiyar mutum.

“Sannan Shan maganin gargajiya da ake yawo da shi a rana na da matsala domin zafin rana ka iya canja sinadarin da aka yi amfani da shi wajen hada maganin wanda hakan ka iya cutar da lafiyar mutum.

“Ya zama dole a rika saka wa masu hada maganin gargajiya ido matuka domin mutane da dama na yin amfani da magungunan ba tare da kula akai ba da sanin illolin da ke tattare da kwankwaɗar su ba yare da an yi taka-tsan-tsan ba.

Adeyeye ta kuma yi kira ga mutane da su guji hada maganin gargajiya da maganin bature domin guje wa samun matsaloli da kiwon lafiyar su.

Share.

game da Author