Hukumar Kwastan ta ce NNPC ke haddasa yawaitar sumogal ɗin fetur kan iyakokin Najeriya

0

Shugaban Hukumar Kwastan ta Ƙasa Hameed Ali, ya ɗora laifin yawaitar sumogal ɗin fetur da ‘yan fasa-ƙwauri ke yi kan Hukumar NNPC.

Ya ce ya sha bayar da shawara ga NNPC ta kafa ƙananan gidajen mai a ƙasashen da ke maƙautaka da Najeriya, amma mahukuntan NNPC ɗin ba su ɗaukar shawarar sa da muhimmanci.

Ali ya yi wannan bayani a taron Kwamitin Majalisar Tarayya mai lura da Harkokin Kuɗaɗe, dangane da Tsarin Kuɗaɗen Shiga tsakanin 2022-2024.

Kwamitin ya ce zai yi amfani da waɗannan kwanakin taro har na tsawon kwana 10 domin yin nazarin bayanan da aka damƙa wa Majalisar Tarayya tun a cikin watan Yuli.

Yayin da ya ke amsa tambaya daga Danmajalisar Tarayya Abdullahi Sa’idu daga Jihar Neja, wanda ya tambayi dalilin da ya sa a kullum ake samun ƙara yawan amfani da fetur a cikin ƙasar nan, Hameed Ali ya ɗora laifin a kan Hukumar NNPC, musamman ɓangaren ta kula da sayar da man fetur, wato DPR.

Shugaban na Kwastan ya ce laifin DPR ne, domin su ke yawan bayar da lasisin gina gidajen sayar da man fetur a garuruwan da ke kusa kan iyakokin ƙasar nan barkatai.

Daga nan sai Ali ya ce idan NNPC ta gina gidajen mai na daffo-daffo ɗin ta a kan iyakokin Najeriya, hakan zai magance matsalar sumogal ɗin fetur kwarai da gaske.

Ya ce tunda farashi ya bambanta daga wuri zuwa wuri, NNPC ta riƙa saidawa a farashi daidai da Najeriya, har da kuɗin ladar safarar fetur ɗin.

“Saboda idan ɗan Jamhuriyar Benin zai iya samun fetur a cikin gidan sa farashi daidai da nan cikin gida Najeriya, sai fa kuɗin safarar man da aka ɗan ɗora masa, to babu abin da zai sa ya riƙa sayen wanda aka yi sumogal aka kai masa a farashin da ya nunka yadda NNPC zai riƙa sayar masa a cikin ƙasar sa.”

“Saboda haka shawara ta har yanzu ita ce idan ana so a magance sumogal ɗin fetur, to NNPC ta kafa gidajen sayar da fetur a waɗannan ƙasashen da ke maƙwautaka da Najeriya.” Inji Hameed Ali.

Share.

game da Author