Kafin Justina Ishaku na zama mai ƙarfin iya noma kadada (hekta) shida a Jihar Nassarawa, asalin ta zaune ta ke a Jihar Kogi, ta na yawon tallace-tallace tsakanin ƙananan garuruwa.
Dama ta fara gajiya da yawon tallar, kuma sai aka yi mata romon-kunne cewa an fi sayen abin da ta ke sayarwa, wato manja a Jihar Nassarawa.
“Na kwashi tarkacen tallar manja na koma Jihar Nassarawa, amma ban daɗe ba sai ɗan jarin nawa ya karye. Daga nan sai na fara kame-kamen wata sana’ar. Sai na koma tallar garin kwaki da shinkafa, nan ma dai babu riba. To daga nan fa na shiga harkar noma kawai.
“Shi noma ya fi yawon tallar manja riba nesa ba kusa ba. Sai fa idan mutum ya ci karo da matsalar tsaro kawai. Saboda tallar da riƙa yi, kasuwannin ƙauyuka na riƙa bi ina yawon tallar. Amma shi noma abu na zama wuri ɗaya.
“Farkon fara harkar noman da na ke yi ban sha wahalar samun gona ba. Wani mutum ya fara ba ni aron kadada biyu a kan naira 25,000 wato shekaru bakwai da su ka wuce kenan. Amma shekarar da ta gabata lamarin ya yi tsada, ya ce sai na biya naira 120,000. Na ce masa kuɗin sun yi yawa. Haka dai ya rage min zuwa naira 80,000, kowace kadada ɗaya naira 40,000 kenan.”
Justina Ishaku ta ce a wajen iyayen ta ta karɓo naira 150,000. Daga nan kuma ta karɓi lamuni daga cibiyoyin bayar wa ƙananan manoma rance.
“Na karɓi bashin naira 350,000, na riƙa biyan kashi 30 bisa 100 duk wata, daga 2013 zuwa 2015.
“Ina noma rogo da gyara. Kuma a kasuwa na ke sayen irin da na ke shukawa. Amma na koma sayen masu inganci da kuwa yalwar ‘ya’ya daga bankin ƙananan manoma. Shi kuma takin zamani wannan mu na zuwa Ofishin Shugaban Ƙaramar Hukuma ana ba mu buhu bi-biyu. Daga nan kuma ina sayen takin kashin shanu da na kashin tsuntsaye.
“Na kan sayi buhu na takin kashin shanu mai nauyin kilogiram 50, naira 2,000. Shi kuma buhun takin kashin tsuntsaye naira 1,000. Na kan yi amfani da buhu 12 na takin kashin tsuntsaye, amma ba ya isa.
“Akwai aikin noman da na ke amfani da masu tarakta. Domin a shekarar da ta gabata, sai da na biya kuɗin hayar masu tarakta naira 300,000 a kwana uku kacal. Amma a noma, mata ne ke min noman ina biyan su naira 40,000. Akwai kuma wasu daga cikin ‘ya’ya na su na taya ni noman.
“Shekarar da ta gabata na haɗu da ƙalubalen zaizayar ƙasa. Wani mai gona ya datse inda ruwa ke bi, don kada ruwa ya yi masa ɓarna a gonar sa. Sai ruwan ya kwararo ta gona ta, ya yi gaba da amfanin gona ta baki ɗaya. To a gaskiya dai zan iya cewa har yanzu ban yi ƙarfi ba a harkar noma.”
Justina ta shaida wa wakilin mu cewa ta na cikin Ƙungiyar Ƙananan Manoma ta Matan Najeriya (SWOFAN). Kuma ta na cikin wata ƙungiyar hada-hada, amma har yau ba ta taɓa taɓa amfanar su ko da buhun takin zamani ɗaya tal ba.
Sannan kuma ta yi kukan yadda wasu ƙwari su ka nemi cinye mata amfanin gona. Sai da ta sayi maganin ƙwari a kasuwa ta fesa. Da kuma yadda aka samu matsalar ƙarancin ruwa sai ta riƙa ɗibar ruwa a ta na yi masu feshin ruwa daga sama.
“Sauƙin da na ke samu wajen sayar da amfanin gona da na ke nomawa, akwai matan da ke zuwa har gona su saye rogon kaf. Sana’ar sarrafa rogo zuwa garin rogo su ke yi.
“Babbar matsala ta dai rashin ƙarfin kuɗi. Idan zan samu tallafi to zan iya ƙara sayen wata gonar. Saboda gona ba matsala ba ce, idan ka na da kuɗin saye.”