HIMMA DAI MATA MANOMA: Idan Hagu Ta Ƙiya A Koma Dama: Yadda na ajiye kwalin digiri na kama harkar noma a Abuja -Blessing, mace mai himma

0

Yayin da wasu da su ka kammala digiri zuwa su shafe shekaru su na karakainar neman aikin gwamnati ko wani aikin da ake samun kuɗi ana zaune cikin ofis mai sanyi, ita kuwa Blessing Iwuofor bayan ta kammala aikin bautar ƙasa, ta ga aikin ba zai samu ba, sai ta ajiye kwalin ta kama harkar noma.

Blessing wadda ta yi digiri a kan Ilmin Tattalin Arziki, da farko dai sai ta nemi aron gona a jihar Nassarawa, kusa da Abuja.

Zaman yanzu ta na noma masara da shinkafa, sannan kuma ta na sarrafa garin wake da garin filanten.

“Tun ina bautar ƙasa na fara sha’awar noma, inda a lokacin na samu aron gona na yi noman doya.

“Lokacin da na ɗebe doya na kai gida, sai na ga ina da muƙa-muƙan doya sun fi 500. Na ce lallai ashe lamarin nan akwai albarka a ciki. Ina maganar tun a cikin 2012 kenan.

“Daga nan na na fara sha’awar noma. Duk da dai bayan na gama aikin bautar ƙasa na so samun aikin da zan riƙa samun kuɗi ina zaune a ofis, amma abin bai yiwu ba.

“Maimakon na riƙa ɓata shekaru neman aiki, sai na kama harkokin noma. Ta kai yanzu baya ga noman da na ke yi, ina sarrafa gari da sauran kayan abincin mata masu ciki da jira-jirai har ma da ƙananan yara.

“Amma da na fahimci lamarin noma a yanzu sai da ‘yan dabaru, na kutsa na shiga ƙungiyon manoma kamar, ‘Community Allied Farmers Association’ of Nigeria da kuma Nigeria Women Agro Allied Farmers Association. Ka san irin waɗannan ƙungiyoyin ne ke taimaka wa mambobin su na samun ramcen kuɗaɗe da tattalin noma. Kuma su na taimaka wa mata manoma su samu gonakin noma.

“Shugabannin ƙungiyoyin ne ke shiga cikin karkara su samu ƙauyukan da ke da gonaki masu yawa sosai. Sai su tsara yadda za a karɓi gonaki aro a tsarin hekta-hekta. Mai noma ce za ta biya kuɗin aron gonar. Idan ki na buƙata to duk shekara sai ki sake biya. Idan kuma daga shekara ɗaya ba ki buƙatar sake biya, to shikenan.”

Blessing ta ce irin wannan noma da ake rainawa wanda mata ke yi, ya na da tasiri sosai a cikin al’umma. Kuma tsarin karɓar aron gona ta ce ya na taimaka wa mata manoma sosai. “Domin za ka iya samun damfareriyar gona ka riƙa nomawa a lungun da a baya ba ka ma taɓa zuwa ba. Ko kuma ka samu inda idan kai kaɗai ka je ka nema, to ba za a taɓa ba ka ba.” Inji ta.

“Yanzu ni ba don irin wannan tsarin ba, ta ya zan samu gona a Nasarawa inda ban san kowa ba?”

Ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa su na ɗaukar hayar masu tarakta su yi masu aikin leburanci, su biya su. Wani aikin kuma majiya ƙarfi ke yi masu da hannu su biya su. Ya dai danganta ga irin yanayin aikin.

“Irin wannan tsarin noma na haɗaka (clusters) da mu ke yi ya na da sauƙi a zamanance. Domin tunda ku na da yawa a tsarin, wasu lokuta ba ka ma buƙatar zuwa gonar.

“Ana raba ranakun zuwa gonar. Idan ku na da yawa, bai fi ka je gonar sau ɗaya ko sau biyu a cikin wata ɗaya ba.

“To hikimar da ake yi, mu na da wani mazaunin ƙauyen wanda ke kular mana da dukkan harkokin noman.

Batun kayan gonar da na ke sarrafawa kuwa, a kasuwa na ke saye, wasu kuma kamar filanten a hannun monoman sa na ke saye. Na fara wannan harkar sarrafa abinci a cikin 2019. Kuma kamar yadda na ke ɗaukar ‘yan aiki a harkar noma. Haka na ke ɗaukar ‘yan aiki a harkar sarrafa kayan abinci.

“Babban ƙalubalen da na ke fuskanta dai bai wuce rashin ƙwaƙƙwaran jari mai kauri ba. Saboda ina buƙatar sayen kayan aiki.”

Share.

game da Author