Hari da daukar fansa ya yi sanadiyyar rayukan ‘yan kabilar Kataf 9, makiyaya 3 a Zangon Kataf

0

Kwamishinan tsaron jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana cewa wasu mahara sun kashe wasu yan kabilar Kataf mazauna kauyen Ungwan Dooh (Mado) dake karamar hukumar Zangon Kataf.

Wadanda aka kashe sun hada da

– Moses Dangana
– Mary Dangana
– Jummai Dangana
– Jerry James
– Happy James
– Endurance Stephen
– Comfort Emmanuel
– Jummai Tanko
– Mary Clement

Jami’an tsaro sun ceto:

– Patrick Chindon
– Joseph Agbon
– Polymer Joseph
– Amos Francis
– Keziah Amos
– Linda Jonathan
– Asabe Jonathan
– Jonathan James
– Lamin Yohanna
– Titi Emmanuel
– Patricia Michael
– Jetral Bala

Sai dai kuma bayan haka mazauna kauyen Dooh, suma sun kai harin ramuwar gayya, inda suka kashe wasu makiyaya 3, suka raunata wasu da dama.
Cikin wadanda suka kashe harda mahaifiyar Ardon, da Kaninsa.

Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna Hadiza Balarabe, ta shaida cewa gwamnati za ta cigaba da samar da tsaroa wadannan yankuna sannan kuma za ta tabbata irin haka bai sake faruwa ba.

A karshe ta mika sakon ta’aziyyarta ga ‘yan uwan wadanda aka kashe.

Share.

game da Author