Gwamnonin jam’iyyar APC sun nemi a gudanar da taron gangami na ƙasa, domin a zaɓar wa jam’iyyar shugabanni, maimakon ci gaba da tafiya a hannun shugaban riƙo, Gwamna Mai-Mala Buni na Jihar Yobe.
Gwamnatin sun fitar da wanann matsaya ta su a cikin wata takardar bayan taron da su ka fitar a ranar Lahadi a Abuja.
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin APC, Abubakar Bagudu na Jihar Kebbi ne ya sa wa takardar hannu, kuma aka raba wa manema labarai a ranar Talata, a Abuja.
An dai naɗa kwamitin riƙon jam’iyya cikin 2020, a ƙarƙashin Gwamna Buni, bayan an tsige shugabancin Odams Oshiomhole.
Takardar sanarwar ta ce gwamnoni sun yi nazarin zaɓen shugabannin mazaɓu da APC ta yi a ranar 31 Ga Agusta. Don haka ta ce ci gaba da sauran zaɓukan a matakai, har a kai ga taron gangamin zaɓen shugabanni na ƙasa baki ɗaya.
Gwamnonin sun yaba tare da jinjina wa shugabancin su Buni musamman yadda aka samu nasarar gudanar zaɓen shugabannin mazaɓu na jam’iyyar lami lafiya, a cikin ruwan-sanyi.
Sun kuma nuna farin cikin yadda Kotun Ƙoli ta jaddada nasarar zaɓen Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu.
Gwamnonin sun kuma ce sun yarda da shugabancin Mai-Mala Buni, ba kamar yadda wasu ke ta yaɗawa ba.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda aka jibge jami’an tsaro a Hedikwatar APC a Abuja.
Sakataren Jam’iyyar APC na Ƙasa, John Akpanudoedehe ya bayyana cewa an jibge jami’an tsaro a Hedikwatar APC da ke Abuja ne domin ƙarfafa tsaro a ofishin na ƙasa.
Da ya ke ganawa da manema labarai a Abuja ranar Litinin, Akpanudoedehe ya ce babu wani abin nuna damuwa ko tayar da hankali.
Ya ce zaratan ‘yan sandan da aka jibge a hedikwatar da ke kan titin Balantire Street, kusa da Barcelona Hotel a Wuse 2 Abuja, an yi kawai domin ƙarfafa tsaro.
“An ƙaro ‘yan sanda ne domin su ƙara wa shugabancin Gwamna Mai-Mala Buni ƙarfin tsaro.
“A duk lokacin da ka tsinkayi alamomin wata matsala ko rahoton wata barazar tsaro, to abu na farko shi ne ɗaukar matakin gaggawa.
“Ba za mu taɓa bari wasu ‘yan tsiraru sun kunyata mu ba, saboda mu ne ke riƙe da gwamnati a ƙasar nan. dalili kenan mu ka ɗauki matakan kariyar duk wata shegantakar da ka iya bijirowa.
“Mun samu rahoton sirri na jami’an tsaro. Don haka ba zai yiwu mu ɗauko ‘yan iska da ‘yan jagaliya su zo su kare Sakateriyar APC ta Ƙasa a Abuja ba. Abin da ya dace shi ne mu sanar wa ‘yan sanda da SSS. Kuma hakan mu ka yi.” Inji Akpanudoedehe.
Idan ba a manta ba ita ma APC ta shiga ruɗani, yayin da wasu jiga-jigan ta su ka nemi Shugaban Riƙo Gwamna Buni ya sauka, domin dokar ƙasa ba ta yarda Gwamna ya riƙe wani muƙami ba.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga rahoton da Karamin Ministan Ƙwadago, Festus Keyamo ya yi gargaɗin cewa mulki zai suɓuce daga hannun APC idan Gwamna Buni ya ci gaba da shugabancin jam’iyyar ko na tsawon sati ɗaya ne.
Ƙaramin Ministan Ƙwadago, Festus Keyamo, ya gargaɗi jam’iyyar APC cewa akwai gagarimar matsalar da ta tunkari jam’iyyar, matsawar Gwamna Mai Mala-Buni na Jihar Yobe ya ci gaba da kasancewa Shugaban Jam’iyya na Riƙo har zuwa jibi Asabar, ranar zaɓe shugabannin APC a matakan Kananan Hukumomi da Jihohi da za’a yi ranar 31 Ga Yuli.
Yayin da ya aika da wata wasiƙar gaggawa ga jam’iyya s asirce, wadda ta faɗo hannun PREMIUM TIMES, Keyamo wanda shi ma gogaggen lauya ne, ya bayyana haramcin riƙe APC da Gwamna Buni ke yi, domin Dokar Ƙasa da Dokar APC sun haramta Gwamna ya riƙe wani muƙami ko shugabanci banda na gwamna da aka rantsar da shi don ya riƙe.
Wannan mahaukaciyar guguwa ta taso ne sanadiyyar hukuncin da Kotun Ƙoli ta Yanke, inda ta jaddada nasarar Gwamna Rotimi Akeredolu na Ondo, na APC, kan Eyitayo Jegede na PDP.
Yadda Sakacin Lauyoyin Jegede Ya Bai Wa Akeredolu Nasara A Ɓagas:
Keyamo ya ce Jegede ɗan takarar PDP ya shigar da Gwamna Akeredolu ƙara, bisa zargin zaɓen da bai cancanta ba, domin a lokacin da aka yi zaɓen cikin Oktoba 2020, Gwamna Mala Buni ne Shugaban Riƙon APC, wanda haramun ne a Dokar Ƙasa Sashe na 183 na 1999 Gwamna ya riƙe wani muƙami daban da na Gwamna.
Haka ma Dokar APC Sashe na 17 ya haramta wa Gwamna riƙe wani muƙami lokacin da ya ke kan mulki.
“Inda Jegede da lauyoyin sa su ka kwafsa shi ne da ba su haɗa da sunan Gwamna Mala Buni Shugaban Riƙon APC tare da na Gwamna Rotimi sun maka su kotu tare ba.
“Da an haɗa da sunan Shugaban Riƙon APC, to da a ranar Litinin Kotun Koli ta soke zaɓen ta bai wa Jegede na PDP nasara.” Inji Keyamo.
A kan haka ne Keyamo ya bada shawarar cewa lallai kamata ya yi a ɗage zaɓen shugabannin APC na Ƙananan Hukumomi da na Jihohi da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar mai zuwa.
“Domin banda Mai Mala-Buni, akwai Gwamnonin Osun da na Neja a cikin Kwamitin Amintattun APC, waɗanda su ma bai kama ta a saka su a ciki ba.
Ya ce idan aka yi zaɓen shugabannin jam’iyya a ƙarƙashin Buni, to duk wanda ya ci zaɓe a ƙarƙashin APC, tun daga kan kansila har shugaban ƙasa sai kotu ta ƙwace kujerar sa.
A kan haka ne ya bada shawara a ɗage zaɓe na shugabannin ƙananan hukumomi da na Jihohi. Sannan a gaggauta cire Mala Buni, ta hanyar taron Majalisar Zartaswar APC na gaggawa, wanda zai cire waɗannan shugabannin riƙo, ya naɗa wasu.
Gwamna Rotimi ya tsallake rijiya ne saboda Alƙalai huɗu daga cikin bakwai ne su ka yarda da zaɓen sa bisa dalilin cewa sun yarda Gwamna Buni bai cancanci riƙe jam’iyya ba, amma mai ƙara fa bai shigar da Buni a cikin ƙarar da ya shigar ba.
Sauran lauyoyi uku kuwa su ka ce ba sai an sha wahalar shigar da sunan Buni ba, tunda dai bai cancanci shugabancin APC ba, to Gwamna Rotimi bai ci zaɓe ba ƙarƙashin APC kenan.
A kan haka ne Keyamo ya ce wannan shari’a ta nuna kenan duk wanda zai kai ƙarar APC nan gaba, to matsawar ya haɗa da sunan Buni, ko tantama babu nasara zai yi a kotu.