Gwamnatin Tarayya ta amince za ta saye hannun jarin kashi 20 bisa 100 na matatar man fetur ɗin da Ɗangote ke ginawa a Legas.
NNPC zai sayi hannun jarin a kan kuɗi dala biliyan 2.76.
Dangote dai ya na kan aikin ginin katafaren matatar mai da kuma sasssfa takin zamani a Legas.
Ƙaramin Ministan Fetur TimipreSylva ne ya bayyana labarin wannan sayen hannun jari a lokacin da ya ke yi wa manema labarai bayani, bayan tashi daga Taron Majalisar Zartaswa, a ranar Laraba, a Fadar Shugaban Ƙasa.
Sannan kuma ya ce Majalisai Zartaswa ta rattaba amincewa da aikin kwangilar gyara matatun mai na Warri da na Kaduna, kan kuɗi dala biliyan 1.5.
“Matatar mai ta Warri za ta lashe dala miliyan 897.66, yayin da matatar Kaduna za ta lashe dala miliyan 586.9
“Za a kasa aikin gyaran matatun Kaduna da Warri zuwa gida uku. Aikin farko cikin watanni 21, aiki na biyu cikin watanni 23. Aiki na uku a kammala ciki wattani 33 baki ɗaya.”
Ya ce tuni an fara aikin gyaran matatar Fatakwal, har an cimma kashi 15 bisa 100 na aikin.