Gwamnatin Tarayya ta fara raba wa marasa galihu tallafin kuɗaɗe a jihohin Kogi da Sokoto

0

Gwamnatin Tarayya ta fara raba wa marasa galihu tallafin naira 20,000 ga mutane 74,000 a Jihar Kogi, a ƙarƙashin Shirin Tura Tallafin Kuɗi ta Asusun Banki (CCT).

Ana raba waɗannan kuɗaɗe ne a ƙarƙashin Shirin Shirin Inganta Rayuwar Marasa Galihu (NSIP).

Haka kuma Gwamnantin Tarayya ta fara wannan aikin rabon kuɗaɗen a Jihar Sokoto.

Shirin CCT dai shiri ne da ake tura wa masara galihu tallafin naira 5,000, wanda Ma’aikatar Agaji, Jinƙai da Inganta Rayuwa ke yi a ƙarƙashin NSIP.

Shugabar Shirin CCT ta Jihar Kogi, Falilat Abdulrazaq ta yi wannan bayani a wurin taron ƙaddamar da rabon kuɗaden, a garin Abocho, cikin Ƙaramar Hukumar Dekina ta Jihar Kogi.

Falilat ta ce maƙasudin bayar da tallafin dai shi ne tabbatar da ganin an cika alƙawarin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi, na fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga ƙangin talauci.

Ta ci gaba da cewa an fara rabon kuɗaɗen tun a ranar Alhamis, inda sama da marasa galihu 7,000 ne kowanen su ya karɓi naira 20,000 .

Falilat ta ce an tsamo waɗanda su ka amfana da tallafin ne daga sassa daban-daban na Ƙaramar Hukumar Dekina.

Ta ce an haɗa wa duk mutum ɗaya tallafin watanni huɗu na naira dubu biyar-biyar daga watannin Janairu, Fabrairu, Maris da kuma Afrilu. Su ne su ka kama naira 20,000 kenan.

Falilat ta ce dukkan ƙananan hukumomi 21 na jihar Kogi sun amfana a baya, kuma a wannan karon ma kowace ƙaramar hukuma za ta amfana.

Ta ce wajen rabon tallafin ana yin la’kari ne da marasa galihun da ba su da halin samun wani abu. Kuma su na amfana tun ma daga horaswar da ake yi masu na kafa hanyoyin dogaro da kai.

“Masu amfana sun koyi dabarun yin tanadin ‘yan kuɗaɗe ta hanyar shiga asusun ajiya daban-daban.

Wasu daga waɗanda su ka amfana sun gode wa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnatin Yahaya Bello na Jihar Kogi.

Yusuf, Agwagwu da kuma Hauwa Musa duk zawarawa ne da su ka amfana daga ƙauyen Elika, Ogbabede da Olowa. Sun gode wa Gwamna Tarayya da ta ba su wannan tallafin da su ka ce zai rage masu raɗaɗin ƙuncin rayuwa sosai.

Rabon Tallafin Marasa Galihu A Sokoto:

Kamar yadda aka fara a Jihar Kogi, an fara rabon kuɗaɗen can a Jihar Sokoto a ƙarƙashin Ofishin CCT da ke jihar.

Babban jami’in shirin Kafar Yabo, wanda ya wakilci Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ne ya ƙaddamar da shirin a garin Tambuwal, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Tambuwal.

Yabo ya ce mutane 3,165 ne za su ci moriyar shirin daga ƙananan hukumomi shida.

Sannan ya ce daga nan kuma za a raba wa wasu mutane har 75,000 naira 20,000 kowanen su, kamar yadda za a yi wa waɗannan su 3,165 ɗin.

Cikin waɗanda su ka amfana a lokacin har da Altine Hassan, Mardiyya Bello da Hassana Isiyaku. Kuma duk sun nuna farin ciki, jin daɗi da kuma godiya ga Gwamnatin Tarayya.

Share.

game da Author