Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na bisa kan gudanar da ayyukan da yanzu haka ake ci gaba da yi har kwangiloli 800 da kuma ginawa da gyaran titina da gadoji masu tsawon kilomita 13, a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Fashola ya yi wannan bayani a lokacin da ya ke duba aikin Gadar Chanchangi da ke cikin Ƙaramar Hukumar Takum a Jihar Taraba.
Ya tabbatar da cewa nan ba da daɗewa ba za a kammala kusan dukkan waɗannan ayyuka domin a samu sauƙin matsalar tsaro, tattalin arzikin ƙasa ya bunƙasa, kuma masu sana’o’i su samu sauƙin gudanar da harkokin su.
Ya kuma ƙara jaddada ƙoƙarin da wannan gwamnati ke yi domin sanin ta kai kwalta mai nagarta ga kowane lungu da saƙo na ƙasar nan. Haka kuma ya ce za a samar da gadoji a duk wuraren da yin hakan ya wajaba.
Daga nan ya roki ‘yan Najeriya su ƙara haƙuri, saboda nan ba da daɗewa ba za a kammala dukkan ayyukan da Gwamnatin Tarayya ke yi a kowace jiha daga cikin dukkan jihohin ƙasar nan 36.
Fashola dai ya yi wannan bayani ne kwana ɗaya bayan ya yi wa ‘yan Najeriya albishir da labarin maido da karɓar kuɗaɗen haraji daga duk wata motar da ta hau manyan titinan gwamnatin tarayya a ƙasar nan. Wannan labari kuwa bai yi wa mafi yawan ‘yan Najeriya daɗi ba.
Fashola ya ce Gwamnatin Tarayya za ta duba yiwuwar karɓar aikin kwalta mai tsawon kilomita 30 daga Takum zuwa Chanchangi, daga hannun Gwamnatin Jihar Taraba.
NAN ta ruwaito cewa Gwamnatin Jihar Taraba ta bayar da aikin ginin titin na Takum zuwa Chanchangi ga kamfanin SCC Nigeria Ltd., amma ɓarkewar cutar korona cikin 2020 ya haifar da matsalar samun kuɗin yin aikin titin.
Fashola ya ce muhimmancin da titin mai tsawon kilomita 30 ke da shi a yankin da ƙasar baki ɗaya ne ya sa Gwamnatin Tarayya ke tunanin karɓar aikin ta yi shi da kan ta.