Gwamnatin Tarayya ta amince a fara gina shingayen karɓar haraji daga motocin haya da waɗanda ba na haya ba a kan manyan titinan Najeriya.
Ministan Ayyuka Raji Fashola ne ya shaida wa manema labarai haka, a Fadar Shugaban Ƙasa, jim kaɗan bayan kammala taron mako-mako na Majalisar Zartaswa (FEC), ranar Laraba, a Abuja.
Fashola ya ce an zartas da sake dawo da karɓar haraji daga masu motocin ne bayan an yi shawarwari da tuntuɓar masu ruwa da tsaki na ciki da wajen gwamnati.
Cikin 2019 ne dai Gwamnatin Buhari ta bayyana aniyar dawo da karɓar kuɗaɗen. Sai dai kuma bisa dukkan alamu ɓarkewar cutar korona a farkon 2020 ya haifar da cikas wajen aiwatarwa a baya.
Fashola ya ce duk da a baya gwamnati ta rushe shingayen karɓar haraji a kan titina, amma dai babu wata doka da ta haramta sake dawo da su.
Ministan ya ce tuni an yi bincike domin yanka farashin kuɗaɗen da ko waɗanne nau’in motoci za su riƙa biya.
Ya ce kuma an tantance wuraren da za a gig-gina shingayen.
“Ba wai daga gobe za a fara karɓa ba, amma dai an cimma babbar matsaya a taron yau Laraba.”
Ya ce za a fara da zaran an kammala gyaran manyan titinan Gwamnantin Tarayya. Kuma a kan manyan titinan ‘Express Way’ kaɗai za a yi.
Fashola ya ce manyan titinan da ke ‘dual carriage’, irin na Kano zuwa Abuja, yawan su ya kai tsawon kilomita 35,000 a faɗin ƙasar nan.
Kananan motoci za su rika biyan biyan naira 200, motocin kasaita wato Jeep, naira 300, Bas-Bas za su rika biyan naira 300, sai kum Bas na haya naira 150 sai kuma Tireloli da manyan motocin Kaya, naira 500.
Discussion about this post