Gwamnati ta datse gadar Gwaram, mahaɗar Kano da jahohin Arewa Maso Gabas ta jiharJigawa

0

Gwamnatin jihar Jigawa ta buƙaci matafiya da suke bin hanyar Gwaram zuwa Basirka da Darazo cewa sakamakon gyara da za’a gudanar a gadar Gwaram an rufe hanyar.

Gadar tana daya daga cikin manya hanyoyi dake hada Jihohin Gombe, Taraba da Adamawa.

A sanarwar da mai baiwa Gwamna sharawa na musamman kan kafafen yada labarai da hulda da jama’a, Habibu Kila yace a yanzu haka babu hanya da manyan motoci zasu rika wucewa.

Kila ya bayar, ta bukaci masu manyan motoci su rika bin hanyar Gwaram sabuwa zuwa Kari, yayinda aka shawarci masu tasowa daga Darazau zuwa Gwaram su rika bin hanyar Kari, Misau zuwa Gwaram Sabuwa har zuwa lokacin da za’a kammala aikin gyaran gadar.

Malam Habibu Nuhu Kila ya ce za’a sanar bude hanyar da zarar an kammala aikin.

PREMIUM TIMES HAUSA ta gano cewa gadar mai shekaru sama da 40 ta samu matsala ne sakamakon ambaliya ruwa a satin da ya wuce.

Share.

game da Author